An Yi Rashi: Hadimin Gwamna Dikko Radda Ya Rasu a Katsina
- An shiga jimami a jihar Katsina bayan rasuwar daya daga cikin hadiman Gwamna Dikko Umaru Radda
- Hon. Nasidi Danladi wanda yake mai ba gwamna shawara kan harkokin ci gaban al'umma ya rasu ne a ranar Asabar, 2 ga watan Agustan 2025
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nuna alhininsa kan rashin da aka yi, wanda ya bayyana a matsayin gwarzon jami'in gwamnati
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana alhini mai zurfi kan rasuwar Hon. Nasidi Danladi Garki.
Marigayin shi ne mai bai wa gwamna shawara na musamman kan ci gaban al’umma, ya rasu ne a ranar Asabar, 2 ga watan Agustan 2025.

Source: Facebook
Babban sakataren yada labaran gwamnan, Ibrahima Kaulaha Mohammed, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin Gwamna Radda ya rasu

Kara karanta wannan
Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano
Marigayi Hon. Nasidi Danladi Garki, wanda ya kasance gwarzon jami’in gwamnati kuma ƙwararren mai haɗa kan jama’a daga matakin ƙasa, ya rasu ne da safiyar Asabar, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Hon. Nasidi Danladi Garki ɗan asalin garin Garki ne da ke cikin karamar hukumar Baure ta jihar Katsina.
Gwamna Radda ya nuna alhininsa kan wannan babban rashi, inda ya siffanta marigayin a matsayin ɗan kishin ƙasa wanda ya yi wa mutanensa da jiharsa hidima cikin tawali’u, aminci, da ƙwazo wajen tallafa wa cigaban al’umma.
"Hon. Nasidi Danladi Garki ba kawai aboki na kusa ba ne, mutum ne mai kishin jihar Katsina."
"A matsayinsa na mai bai wa gwamna shawara kan ci gaban al’umma, ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da jawo jama'a, musamman ‘yan karkara, cikin harkokin gwamnati da aiwatar da ayyukan cigaba.”
"Rasuwarsa babban gibi ne ga wannan gwamnati, ga iyalansa da kuma duk wanda suka samu damar aiki tare da shi."
- Gwamna Dikko Radda
Gwamna Radda ya kara da cewa marigayi Nasidi Danladi Garki ya taka muhimmiyar rawa wajen rage gibin da ke tsakanin gwamnati da al’umma, musamman a fannonin ƙarfafa al’umma da shirye-shiryen wayar da kan jama’a karkashin wannan gwamnati.

Kara karanta wannan
Bayan saɓani ya shiga tsakani, Shugaba Tinubu ya gana da na hannun daman Kwankwaso
Gwamnan ya roƙi Allah (SWT) da Ya gafarta masa, Ya karɓi ayyukan alherinsa, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.

Source: Facebook
Gwamnan Katsina Radda ya yi ta'aziyya
Haka zalika, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, jama’ar karamar hukumar Baure, da dukkan al’ummar jihar Katsina baki ɗaya.
"A madadin gwamnatin jihar Katsina da al’ummar ta, muna mika gaisuwar ta’aziyya. Allah Ya ba iyalansa da masoyansa haƙuri da ƙarfin zuciya a wannan lokaci mai tsanani."
- Gwamna Dikko Radda
Gwamnatin jihar Katsina za ta gyara asibitoci
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta shirya kashe kudade don gina katangu a wasu asibitoci saboda matsalar tsaro.
Gwamnatin za ta kashe N703m don sake gina katangu a manyan asibitoci da ke kananan hukumomi 14 na jihar.
Kwamishinan ayyuka na jihar ya bayyana cewa za a yi ayyukan ne a kananan hukumomin da ke fama da rashin tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng