Kabiru Gombe Ya Caccaki Sheikh Jingir bayan Malaman Izalar Jos da Kaduna Sun Hadu
- Sheikh Kabiru Gombe ya soki Sheikh Sani Yahaya Jingir kan zargin Peter Obi da al’ummar Ibo game da kisan Sardaunan Sokoto
- Caccakar ta biyo bayan ziyarar Obi ga mataimakin shugaban majalisar malamai na Jibwis, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun
- Malaman Izalar Jos da Kaduna sun hadu a daurin aure da wa’azin walima a Katsina karkashin jagorancin Sheikh Yakubu Musa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina –Sheikh Kabiru Haruna Gombe, ya nuna rashin jin daɗinsa kan furucin Sheikh Sani Yahaya Jingir game da ziyarar da Peter Obi ya kai gidan Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun.
Furucin ya janyo ce-ce-ku-ce bayan wani wa’azi da Sheikh Jingir ya yi yana jingina Peter Obi da kabilar sa da kisan Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Sheikh Kabiru Gombe ya yi ne a cikin wani sako da shafin Jibwis Nigeria ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana cewa irin wannan zargi ba shi da tushe kuma bai dacewa da hali na malami.
"Zargin bai kamata ba" — Kabiru Gombe
Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana cewa bai kamata a jingina laifi ga wanda bai aikata shi ba saboda wani dan kabilarsa ya aikata laifin.
A cewarsa, ziyarar da Peter Obi ya kai gidan Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ba wani laifi ba ne balle ta zama dalili na kawo rabuwar kai ko suka.
Ya bayyana cewa Sardaunan Sokoto da kan shi ba ya nuna gaba ko kiyayya ga wasu, kuma duk wanda ya yi haka ba da shi ya yi koyi ba.
Malaman Izala sun ziyarci jihar Katsina
A lokaci guda kuma, an gudanar da babban taron da ya hada malaman Izalar Jos da Kaduna a birnin Katsina.
Jibwis Katsina ta wallafa a Facebook cewa taron ya hada da daurin aure da wa’azin walima na ‘ya’yan Sheikh Yakubu Musa, wato Salwa Yakubu Musa da Ummu Sulaim Mujtaba Yakubu.
Shugaban Jibwis na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da mataimakin Sheikh Jingir, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun, sun halarci taron tare da sauran manyan malamai.

Source: Facebook
Wa'azin walima da jawaban malamai
Wa’azin walimar maza ya gudana ne a Masallacin Zaid Bin Thabit, yayin da mata suka yi nasu washegari a masallacin.
Alarammomi kamar su Abubakar Adam Katsina, Ahmad Sulaiman Kano da Nasiru Salihu Gwandu sun gabatar da karatun Alƙur'ani mai tsarki.
Malaman da suka yi wa’azi sun yi kira da zaman lafiya da girmama juna a tsakanin al’ummar musulmi a Najeriya da duniya baki daya.
Malami ya fassara Kur'ani zuwa Yarbanci
A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addinin Musulunci mai suna Dr Dauda Awwal ya yi sabon fassarar Al-Kur'ani mai girma.
Malamin ya bayyana cewa ya yi amfani da harsuna da suka hada da Yarbanci da Turanci wajen fassarar.
Dr Awwal ya tabbatar da cewa ya shafe sama da shekara 20 yana aikin, kuma yana rokon da a taimaka wajen buga littafin da yada shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

