Jagororin 'Yan Bindiga Sun Gwabza Fada a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka
- An samu barkewar wani mummunan rikici tsakanin wasu jagororin 'yan bindiga masu gaba da juna a jihar Zamfara
- Lamarin ya auku ne bayan da fada ya barke tsakanin 'yan bindigan a wani kauye da ke karamar hukumar Tsafe
- Rikicin ya yi sanadiyyar hallaka wani jagoran 'yan bindiga da wasu mataimakansa bayan an kai musu hari hari har gida
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Wani mummunan rikici ya barke tsakanin wasu manyan jagororin ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Rikicin da ya barke a karamar hukumar Tsafe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, bayan an yi mummunan arangama.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagororin 'yan bindiga sun gwabza fada
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa rikicin ya faru ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Yulin 2025 a ƙauyen Marbe da ke cikin yankin Kwaren Ganuwa.

Kara karanta wannan
"Ba mu buƙatar kuɗi," Kasurgumin ɗan bindiga, Sani Black ya zo da sabon salo a Zamfara
Rikicin ya auku ne lokacin da ƴan bindiga masu biyayya ga Kachalla Alti wani sanannen jagoran ƴan bindiga suka kai hari gidan abokin gabarsa, Haruna Hari.
Bayanai sun nuna cewa harin ya fara ne da misalin ƙarfe 11:15 na safe, inda hakan ya haifar da mutuwar Haruna Hari da wasu mataimakansa guda biyu.
Maharan sun kuma sace adadi mai yawa na shanu da kuma makaman da marigayi Haruna ya mallaka, kafin su tsere zuwa wani wuri da ba a san shi ba.
Wannan lamari wani ɓangare ne na rikicin da ya jima yana gudana tsakanin ɓangarorin biyu, inda suka sha yin artabu domin samun iko da hanyoyin aikata laifi da kuma gudanar da hare-hare a yankin.
Wani mazaunin yankin Kwaren Ganuwa ya bayyana cewa dama sun saba yin rikici a tsakaninsu.
"Ba wannan ne karo na farko da suka yi artabu ba, amma wannan shi ne mafi muni. Mutanen wannan yankin sun daɗe suna rayuwa a cikin fargaba da tsoron waɗannan gungun ƴan bindiga.”
- Wani mazaunin yankin
Ana fada tsakanin 'yan bindiga a Zamfara
Ko da yake ba a samu rahoton mutuwar farar hula ba, rikicin cikin gida tsakanin gungun ƴan bindiga a Zamfara yana ƙaruwa cikin watannin baya-bayan nan.

Source: Original
Rikicin na faruwa ne musamman sakamakon ƙoƙarin mamaye yankuna, samun makamai da kuma karɓar kuɗin fansa.
Kisan Haruna Hari na iya janyo harin ramuwar gayya nan gaba, musamman a yankunan Tsafe da Maradun inda duka bangarorin ke da ƙarfi da kuma tasiri.
'Yan bindiga sun yanka mutane a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun yi wa mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba yankar rago a jihar Zamfara.
Miyagun sun tafka wannan mumunar ta'asar ne a kauyen Banga da ke cikin karamar hukumar Kauran Namoda.
Shugaban karamar hukumar, wanda ya yi karin haske kan lamarin ya bayyana cewa mutanen da aka yanka na daga cikin wadanda aka sace wasu watanni da suka gabata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
