Kano, Kaduna da Sauran Jihohin Najeriya da Ruwa Ya Yi Ajalin Mutane 165 a 2025

Kano, Kaduna da Sauran Jihohin Najeriya da Ruwa Ya Yi Ajalin Mutane 165 a 2025

  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya (NEM) ta fitar da alƙaluman asarar da aka yi sakamakon ambaliyar ruwa a shekarar 2025
  • Rahoto ya nuna cewa aƙalla mutane 175 ne aka tabbatar sun mutu, wasu 82 suka ɓata a ambaliyar ruwan da ta afku a jihohi 19
  • NEMA ta bayyana cewa mutane 119,791 ne ambaliyar ta shafa kuma mafi yawancinsu mata ne da ƙananan yara a shekarar bana

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sababbin alkaluman da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta fitar sun bayyana irin asarar rayuka da ambaliya ruwan ta haddasa a 2025.

Legit Hausa ta ruwaito cewa daga watan Janairu zuwa watan Yuli, 2025, an samu asarar ɗaruruwan rayuka a jihohin Najeriya samakon ambaliyar ruwa.

Ambaliyar ruwa a Najeriya.
Mutane 165 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a 2025 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa rahoton NEMA ya nuna cewa an rasa rayuka da dukiyoyi masu dumɓin yawa sakamakon ɓallewar ruwa a jihohin Kudu da Arewa.

Kara karanta wannan

Ba sauki: Dakarun sojoji sun hallaka manyan kwamandojin 'yan ta'adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambaliya ta kashe mutane 165 a Najeriya

A alkaluman asarar da aka tafka sanadiyyar ambaliya, NEMA ta bayyana cewa an tabbatar da mutuwar mutane 165, yayin da wasu 82 ke bata har yanzu ba a gansu ba.

NEMA ta tattara cewa ambaliyar ruwa ta shafi mutane 119,791 a fadin jihohi 19 na ƙasar nan ciki har da Kano da Kaduna.

Sababbin alkaluman da hukumar NEMA ta fitar a ranar Juma’a sun kuma nuna irin girman barazana da ambaliyar ta haifar, da kuma adadin mutanen da suka rasa matsuguni ko dukiyoyinsu.

Yadda ruwa ya lalata gidaje da gonaki

A cewar rahoton halin da ambaliya ta jefa mutane a 2025:

“Mutane 138 sun jikkata da raunuka daban-daban, 43,936 sun rasa matsuguni, gidaje 8,594 sun rushe, yayin da gonaki 8,278 suka lalace a kananan hukumomi 43 a jihohi 19.”

Rahoton ya ƙara da cewa ƙananan yara da mata ne suka fi yawa cikin waɗanda ibtila'in ambaliyar ruwa ya shafa, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Kara karanta wannan

Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya

A cewar bayanan:

“Yara 53,314, mata 36,573, maza 24,600, tsofaffi 5,304 da kuma masu nakasa 1,863 ne ambaliya ta shafa a bana. Jihohin da ke da mafi yawan mutane da ambaliya ta shafa su ne: Imo, Ribas, Abia, Borno da Kaduna.”

Jerin jihohin da aka yi ambaliya a 2025

Jihohin da ambaliyar ruwan ta yi ɓarana a bana sun haɗa da:

1. Jihar Abia

2. Jihar Adamawa

3. Jihar Akwa Ibom

4. Jihar Anambra

5. Jihar Bayelsa

6. Jihar Borno

7. Jihar Edo

8. Jihar Gombe

9. Jihar Imo

10. Jihar Jigawa

11. Jihar Kaduna

12. Jihar Kano

13. Jihar Kogi

14. Jihar Kwara

15. Jihar Neja

16. Jihar Ondo

17. Jihar Ribas

18. Jihar Sakkwato da

19. Birnin tarayya, Abuja.

Ambaliya ta yi ɓarna a jihohin Najeriya.
Hukumar NEMA ta bayyana cewa mata da ƙananan yara ambaliyar ta fi yiwa illa Hoto: Getty Image
Source: Facebook

Jerin jihohin da ake hasashen ambaliyar ruwa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ambaci lokacin da ambaliyar ruwa zai yi ƙamari saboda al'ummar Najeriya su shirya kuma su ɗauki matakan kare kai.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da kashe sama da N712bn a yi wa filin jirgin Legas kwaskwarima

Gwamnatin ta lissafo jihohi 19 inda ake hasashen za a samu ambaliyar ruwa mai muni a a faɗin kasar nan a daminar bana.

Ministan ruwa da tsaftar muhalli, Farfesa Joseph Utsev ne ya bayyana hakan, ya ce ambaliyar ruwan za ta faru ne saboda mamakon ruwa da za a rika yi da kuma toshe magudanar ruwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262