Ba Sauki: Dakarun Sojoji Sun Hallaka Manyan Kwamandojin 'Yan Ta'adda
- Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana nasarorin da dakarun sojojin Najeriya suka samu kan 'yan ta'adda
- Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan kwamandojin 'yan ta'adda a sassa daban-daban na kasar nan
- DHQ ta bayyana cewa sojojin sun kuma cafke 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuffuka masu yawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana nasarorin da dakarun da ke fafutukar kawar da ‘yan ta’adda da sauran miyagun laifuka a sassan ƙasar nan suka samu.
Hedikwatar ta bayyana cewa sojojin sun hallaka kwamandoji biyar da ake nema ruwa a jallo a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Source: Twitter
Daraktan Hulɗa da jama’a na DHQ, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana hakan ga manema labarai, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan
Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kashe kwamandojin 'yan ta'adda
Ya bayyana cewa kwamandojin da aka kashe sun haɗa da Amir Dunkei, Kachalla Nagomma, Gurmu, Ali Yar Daribiyar, da Yello Dambokolo.
Hakazalika ya bayyana cewa wasu fitattun masu safarar makamai da masu garkuwa da mutane da ke cikin jerin sunayen wadanda ake nema sun shiga hannu, kuma an damƙe su domin gudanar da bincike.
Wadanda aka kama sun haɗa da: Yakubu Jubril, Abubakar Yahaya, Isiya Sani, Haruna Abdullahi Ali Abba da Mallam Aminu Idris.
Har ila yau akwai Mohammed Hamisu (wanda aka fi sani da Mamiyo ko Officer Mohammed), Shuaibu Bulama, Isah Abdullahi da kuma Abdullahi Mohammed.
"Daga cikin shahararrun ‘yan ta’adda da aka kashe akwai masu matsanancin mugunta da rikici irin su Prince Justin Ishimiri da kuma wani fitaccen shugaban kungiyar masu tsattsauran ra’ayi, Liamdoo Douglas Adekpe (wanda aka fi sani da Bajor)."
- Manjo Janar Markus Kangye
Hakazalika, ya bayyana cewa a cikin watan Yuli na shekarar 2025, dakaru a fagen daga sun kashe adadi mai yawa na ‘yan ta’adda, sun kama mutum 578 da ake zargi da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka, rahoton TheCable ya tabbatar.

Source: Twitter
Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram
"Dakarun Operation Hadin Kai sun gudanar da hare-hare masu amfani kan ‘yan Boko Haram da ISWAP a yankunan Marte, Bula Daburu, Alau Dam, Limankara, Bitta, Kawuri da ƙauyen Monguno."
"An kai hare-haren ne a kananan hukumomin Marte, Bama, Konduga, Kaga, Gwoza da Guzamala na jihar Borno da kuma ƙauyen Mildo a karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa."
"Sun kashe ‘yan ta’adda da dama, sun kama guda takwas sannan suka ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su."
- Manjo Janar Markus Kangye
Boko Haram: Sojoji sun kashe 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.
Sojojin sun hallaka 'yan ta'addan na Boko Haram ne a kauyen Bula Dabaru da ke karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Dakarun sojojin sun hallaka 'yan ta'adda biyu tare da raunata wasu da dama bayan sun yi zazzafan musayar wuta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
