Dangote Ya Fara Cin Karo da Matsala, Ana Fargabar Zai Jawo Karancin Mai
- Ƙungiyar dillalan mai ta NOGASA ta ce shirin Aliko Dangote na rarraba man fetur kai tsaye zai iya haddasa karancin man fetur
- Shugaban NOGASA ya ce rashin haɗin gwiwar Dangote da yayan kungiyar na iya tilasta musu daina aiki gaba ɗaya
- Ƙungiyar ta bukaci Bola Tinubu ya shiga tsakani, don tabbatar da adalci da daidaito tsakanin masana'antun da masu rarraba mai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ƙungiyar dillalan mai ta NOGASA ta yi magana kan shirin attajiri Aliko Dangote na rarraba man fetur kai tsaye.
Kungiyar ta ce hakan zai iya haddasa karancin man fetur a ƙasar baki daya duba da halin da ake ciki a yanzu.

Source: Getty Images
An fadi abin da Dangote ke son jawowa Najeriya
Shugaban NOGASA, Benneth Korie, ya bayyana hakan a babban taronsu da aka gudanar a Abuja, inda ya ce Dangote bai tuntubi mambobinsu ba game da shirin, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce rashin haɗin gwiwar Dangote da mambobinsu na iya tilasta musu daina aiki gaba ɗaya domin ya ɗauki ragamar kasuwa
Hakan na zuwa ne kasa da makonni biyu kafin matatar Dangote ta fara rarraba man fetur kai tsaye, The Guardian ta ruwaito.
Korie ya bayyana cewa idan aka ci gaba da haka, mambobin ƙungiyar za su dakatar da aiki, su bar Dangote shi kaɗai ya sarrafa kuma ya rarraba man.
Ya jaddada cewa ba sa adawa da nasarar masana'antar Dangote, amma ya ce kamfanin na ɗaukar hanyar da ta durƙusar da matatun NNPCL.

Source: UGC
Dangote: Rokon dillalan mai ga Shugaba Tinubu
Shugaban NOGASA ya bukaci Shugaba Tinubu da ya sa baki, ya ce Dangote ya bi ƙa’ida don ka da a tauye wa sauran haƙƙoƙin kasuwanci.
Ya ce mafi muhimmanci a yanzu shi ne Dangote ya maida hankali wajen sarrafa man sosai, ya sayar da shi ga dillalan su rarraba.

Kara karanta wannan
Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya
Ya ce:
“Idan kamfanin Dangote na da ma’aikata 1,000, mu muna da fiye da 4,000 da ke dogaro da wannan aiki."
Ya kara da cewa matakin na Dangote zai sa mutane da dama rasa ayyukansu, kuma akwai yiwuwar ba 'yan Najeriya ne ke aiki da shi gaba ɗaya ba.
Shi ma shugaban ƙungiyar PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya ce yawancin 'yan ƙasa ba su fahimci haɗarin da ke tattare da wannan sabon shirin ba.
Sun bukaci gwamnati ta tabbatar da adalci a kasuwar mai, inda kowa zai samu damar cin moriyar tsarin ba tare da danniya ba.
Dangote zai saka matatarsa a kasuwa
Kun ji cewa Aliko Dangote ya ce nan ba da jimawa ba zai sa matatarsa ta mai a kasuwa domin 'yan Najeriya su mallaki hannun jari.
Ya bayyana cewa matatar tana samar da tan 2,500 na iskar gas a rana domin bunkasa amfani da makamashi wajen girki.
Dangote ya karyata zargin neman mamaye harkar man fetur, yana mai cewa ya fi so ya zuba jari a Najeriya ba a wasu kasashen waje ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
