Shugaba Tinubu Ya Taɓo Mutanen Ganduje, Ya Maye Gurbin Gawuna a Jami'ar BUK
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire Dr. Nasir Yusuf Gawuna daga muƙamin da ya naɗa shi na farko a Jami'ar Bayero da ke Kano watau BUK
- A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar yau Juma'a, Tinubu ya ce ya sauya Gawuna ne domin ba shi damar maida hankali a hukumar FHA
- Bola Tinubu ya maye gurbin shi da Air Vice Marshal Saddiq Ismaila Kaita (mai ritaya) domin ci gaba da kula da harkokin gudanarwar jami'ar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Air Vice Marshal Saddiq Ismaila Kaita (mai ritaya) a matsayin sabon Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK).
AVM Kaita ya maye gurbin tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, wanda shugaban ya naɗa a mukamin Shugaban Hukumar Gidaje ta Ƙasa (FHA).

Source: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a yau Juma'a, 1 ga watan Agusta, 2025, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Tinubu ya ba Gawuna muƙamai 2
Idan baku manta ba, Tinubu ya naɗa Gawuna, ɗaya daga cikin na hannun daman tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban Majalisar Gudanarwa ta Jami'ar BUK.
Makonni bayan hakan kuma Tinubu ya sake naɗa Gawuna a matsayin shugaban hukumar kula da harkokin gidaje ta ƙasa (FHA), lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.
Shugaba Tinubu ya maye gurbin Gawuna a BUK
A cewar sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar yau Juma’a, shugaban ƙasa maye gurbin Gawuna da AVM Kaita a Majalisar Gudanarwa ta Jami'ar BUK.
Sanarwar ta ce Bola Tinubu ya yi wannan sauyi ne domin bai wa Dr. Gawuna damar mayar da hankali kan aikin sa a Hukumar FHA, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano

Source: Facebook
Taƙaitaccen bayani kan AVM Kaita
Kafin ya yi ritaya daga Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, AVM Saddiq Ismaila Kaita ya rike mukaman Daraktan Tsare-tsare a Hedikwatar Tsaro (DHQ) da Shugaban Sashen Sauyi da Ƙirƙira na Rundunar Tsaro.
Sanarwar ta ƙara da cewa AVM Kaita jajirtacce ne wanda ya ba da gudunmawa a fannin horarwa da daidaita matakai daban-daban a cikin Sojin Sama.
“Kafin ya yi ritaya daga Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, AVM Saddiq Ismaila Kaita ya rike muƙamin Daraktan Tsare-tsare a Hedikwatar Tsaro (DHQ) da muƙamin Shugaban Sashen Sauyi da Ƙirƙira na Rundunar Tsaro."
“Ya kuma yi ƙaurin suna saboda gudunmawar da ya bayar a fannin horarwa da daidaita tsarin aiki a cikin Rundunar Sojin Sama,” inji sanarwar.
Shugaba Tinubu ya ba ɗan IBB muƙami
A wani rahoton, kun ji cewa Bola Tinubu ya naɗa Muhammad Babangida ya zama shugaban Bankin Noma, wanda aka farfaɗo da shi domin ƙarfafa tattalin arzikin gona.
Wannan naɗin dai na ɗaya daga cikin naɗe-naɗe takwas da Shugaba Tinubu ya amince da su, wanda ya haɗa da shugabannin wasu hukumomin gwamnati.
Babangida, ɗan tsohon shugaban soja, Ibrahim Babangida, ya na da ilimi mai zurfi daga jami’ar Turai da makarantar kasuwanci ta Harvard.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

