INEC Ta Fara Shirin 2027, za a Fara Rajistar Masu Zabe a Jihohi 36
- Hukumar zabe mai ta kasa, INEC za ta fara rijistar masu kada kuri’a ta yanar gizo a ranar 18 ga watan Agusta, 2025
- Wannan matakin yana daga cikin shirye-shiryen zaben gwamna a Anambra da kuma babban zaben 2027
- Hukumomin INEC da NOA sun sake jaddada hadin kai don fadakar da jama’a da kuma amfani da fasahar zamani
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa za ta fara gudanar da rijistar masu kada kuri’a ta yanar gizo a fadin kasar nan daga ranar 18 ga watan Agusta, 2025.
Wannan matakin zai kasance wani bangare na shirin ci gaba da rijistar masu zabe (CVR) kafin babban zaben shekarar 2027.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan yadda za a fara rajistar masu zabe ne a cikin wani sako da INEC ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar INEC za ta fara rajistar masu zabe
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce za a fara rajistar masu zabe yayin wata ziyarar bangirma da shugabannin Hukumar Wayar da Kai ta NOA suka kai ofishinsa da ke Abuja.
Ya bayyana cewa rijistar yanar gizon za ta kasance wani mataki na farko a cikin shirye-shiryen da ake yi na gudanar da zaben gwamna a Jihar Anambra da zaben 2027.
Rahoto ya nuna cewa an shirya gudanar da zaben Anambra ne a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025.
INEC za ta hada kai da NOA
Farfesa Yakubu ya ce hadin gwiwa da NOA yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da cewa jama’a musamman matasa da mata sun samu cikakken bayani da fadakarwa.
Ya yabawa NOA bisa yadda take amfani da kafafen sadarwa na zamani kamar NOA TV, NOA Radiyo da kuma sabuwar manhajar AI ta CLHEEAN.
Daily Trust ta wallafa cewa shugaban INEC ya ce:
“Hadin gwiwa tsakanin INEC da NOA yana da matukar amfani. Wayar da kai na bukatar kafafe da dama kuma NOA na da dukkan hanyoyin da suka dace.”
Ya kara da cewa INEC ta kuduri aniyar karfafa hadin gwiwa da kungiyoyin fararen hula, jam’iyyu da kafafen yada labarai domin karfafa shiga harkar zabe, musamman ga mata da matasa.

Source: Twitter
NOA za ta taimakawa hukumar INEC
A nasa jawabin, Darakta Janar na NOA, Lanre Issa-Onilu, ya ce hukumar sa tana cikin yin gyare-gyare domin inganta aikin wayar da kai da kuma ilimantar da jama’a kan dimokuradiyya.
Ya ce lokacin da ya karbi ragamar hukumar, akwai sassa guda uku da ke kula da shirye-shiryen, amma yanzu akwai sassa 16.
Hukumar INEC ta jaddada cewa za ta ci gaba da hada kai da NOA domin tabbatar da cewa rijistar masu zabe da sauran ayyukan zabe sun gudana cikin nasara a duk fadin kasar.
An gargadi INEC kan zaben 2027
A wani rahoton, kun ji cewa, daya daga cikin dattawan Arewa, Dr Hakeem Baba Ahmed ya yi gargadi kan zaben 2027.
Dr Hakeem Baba ya bayyana cewa magudin zabe a shekarar 2027 zai iya jawo babbar fitina a Najeriya.
Dattijon ya bukaci hukumar INEC da 'yan siyasa sun kaucewa son zuciya wajen tattabar da an yi sahihin zabe domin tabbatar da zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


