Masana'antar Fina Finan Najeriya Ta Yi Rashi, Matashiyar Jaruma Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Fitacciyar jarumar Nollywood da ke tashe, Omotola Odunsi ta riga mu gidan gaskiya ranar Alhamis, 31 ga watan Yuli, 2025
- Abokan aiki da jarumai a masana'antar shirya fina-finan da ke Kudancin Najeriya sun tabbatar da mutuwarta a sakonni daban-daban
- Sun bayyana alhini da jimaminsu bisa wannan rashi da suka yi tare da addu'ar Allah Ya ba iyalanta haƙuri da juriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Fitacciyar Jarumar masana'antar shirya fina-finan Nollywood, Omotola Odunsi, ta riga mu gidan gaskiya.
Ɗaya daga cikin abokanan aikinta, Akinola ‘Segbowe’ Akano ne ya tabbatar da rasuwar fitacciyar jarumar.

Source: Instagram
Ya sanar da mutuwar ne a cikin wani saƙon alhini da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, 31 ga watan Yuli, 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da rasuwar jarumar Nollywood

Kara karanta wannan
Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano
Akinola ya bayyana tattaunawar da ya yi da marigayiyar ta ƙarshe tare da hotunanta, inda ya bayyana cewa kafin rasuwarta ta faɗa masa ta samu sauƙi.
“Motola! Abin mamaki amma na ƙoƙarta na tuntube ki da sassafe kuma kin ce kina murmurewa. Wannan labari ne mai matuƙar girgiza. Omotola! Ki huta lafiya, ƙanwata. Allah ya jikan ki, ya kuma taimaki iyalanki,” in ji shi.
Har kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan ciwo ko wani dalili da ya zama ajalin jarumar, wacce ke jan zarenta a Nollywood.
Fitaccen jarumi Odunlade Adekola, wanda ya horar da ita a masana'antar fina-finai, ya tabbatar da rasuwarta a shafinsa na Instagram, da cewa, "R.I.P Omotola."
Jaruman Nollywood sun yi alhinin mutuwar
Haka zalika, jaruma kuma uwar ɗan mawaki, Portable, wato Ashabi Simple, ta bayyana alhini kan rasuwar Omotola.
Ta tuna yadda suka haɗu a ɗaya daga cikin fina-finan da aka yi kwanan nan kuma suka yi niyyar yin aiki tare nan gaba.
“Na firgita sosai. Kin kasance ɗaya daga cikin fitattun jaruman da nake fatan su ƙara ɗaukaka. Mun haɗu tun farkon shekarar nan a lokacin da nake fim ɗin ‘Deputy’ kuma mun yi alkawarin yin fim tare a gaba.
"Sai ga shi, kin tafi ba ki jira ki ga sakamako ba. Ina tuna yadda kike ba ni shawarwari da ƙarfafa gwiwa. Yawancin burinki ma ba su cika ba.
"Ya Allah, ba za mu iya tuhumarka ba. Mutuwa ba ƙaramin abu ba ne,” in ji ta.

Source: Instagram
Yadda Jaruma Omotola ta shiga harkar fim
Omotola ta fara aiki a matsayin jami’ar kula da harkokin bashi a wani banki kafin ta yi murabus a shekarar 2019 domin bin burinta na yin fim, rahoton Tribune.
A 2018, ta yi nasarar shiga kamfanin Odunlade Adekola Films Production, inda ta fara aikinta na farko a fagen shirya fina-finai karkashin kulawar fitaccen jarumi Odunlade Adekola.
An rasa jaruma a Nollywood
A wani labarin, kun ji cewa jaruma a masana'antar Nollywood kuma ƴar gwagwarmayar kare haƙƙin mata masu ƙiba a Najeriya, Monalisa Stephen ta mutu.
Jarumar wacce ta shahara a ɓangaraen harkar fim da harkokin soshiyal midiya ta mutu ne sakamakon rashin lafiya.
Monalisa, mai shekara 33 a duniya, ta shahara wajen kare hakkokin mata masu jiki watau mata masu ƙiba da kuma wayar da kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
