ASUU, SSANU: Ma'aikatan Jami'a Sun Fusata, Sun Shiga Yajin Aikin sai Baba Ta Gani
- Kungiyoyin ASUU, SSANU, NASU da NAAT sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a jami’ar LASU daga Alhamis, 31 ga Yuli, 2025
- An umarci malamai da ma’aikata da su janye daga aiki a LASU, LASUCOM-Ikeja da sashen Epe har sai an biya bukatun kungiyoyin
- Bukatun sun hada da karin albashi, daidaita albashi da na sauran makarantu da kuma aiwatar da sabon mafi karancin albashi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Kungiyoyin malamai da ma'aikatan jami'o'in Najeriya sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Alhamis, 31 ga Yulin 2025.
Wannan yajin aikin dai ya shafi malamai da ma'aikatan jami'ar jihar Legas (LASU) sakamakon wasu matsalolin jami'ar da aka gaza magancewa.

Asali: Twitter
ASUU, SSANU, NASU sun shiga yajin aiki
Jaridar Punch ta rahoto cewa kwamitin kungiyoyin da suka shiga yajin aikin sun hada da ASUU, SSANU, NASU da kuma NAAT.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gamayyar kungiyoyin sun sanar da wannan matakin na shiga yajin aikin a wasikar da suka fitar a ranar Alhamis, wacce aka aikewa shugaban jami'ar, Prof. Ibiyemi Olatunji-Bello.
Wasikar na dauke da sa hannun shugaba da sakataren kungiyar ASUU-LASU, Prof. Ibrahim A. Bakare and Sylvester O. Idowu, da kuma shugaba da sakataren SSANU-LASU, Oluwaseyi Lawal and Waheed Majekodunmi.
Wasikar ta umarci dukkanin malamai da ma'aikatan jami'ar da ma na kwalejin koyon aikin likitanci na jami'ar (LASUCOM-Ikeja) da kuma sashen jami'ar na Epe da su janye ayyukansu nan take.
An umarci ma'aikata su bar wuraren aiki
Jaridar Vanguard ta rahoto wani bangare na wasikar na cewa:
"‘Bisa ga shawarar da aka cimmawa a taron gaggawa na kwamitin haɗin gwiwar kungiyoyin ASUU-LASU, SSANU-LASU, NAAT-LASU da NASU-LASU, cewa ya kamata a fara yajin aiki na sai baba-ta-gani daga ranar Alhamis 31 ga Yuli, 2025, mun rubuta wannan takardar don sanar da ku cewa yajin aikin ya fara aiki nan take.
“Yajin aikin zai ci gaba har sai hukumomin da abin ya shafa sun biya dukkan buƙatun ma’aikatan jami'ar.
“Da wannan ake umartar dukkanin malamai da ma’aikatan jami’ar da na rassan kwalejojinta (LASUCOM da LASU-Epe) da su janye ayyukansu tare da barin wuraren aikin nan take."

Asali: Getty Images
Wasu bukatun ma'aikatan jami'ar Legas
A halin da ake ciki, an ruwaito cewa ɗaliban jami’ar na shirin fara jarrabawar zango na biyu na shekarar 2024/2025 a ranar Litinin mai zuwa, sai ga shi an fara yajin aikin.
Wasu daga cikin bukatun ma'aikatan sun hada da aiwatar da karin albashi na kashi 25 zuwa 35.
Sauran bukatun sun hada da daidaita albashin malamai da ma'aikatan jami'ar LASU da na sauran manyan makarantu mallakin jihar.
Hakazalika, sun bukaci a aiwatar da sabon mafi karancin albashi da Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu a baya.
Malaman asibiti sun shiga yajin aiki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, akalla malaman jinya 25,000 karkashin kungiyar NANNM ne suka tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai.
Yajin aikin zai shafi dukkanin asibitocin gwamnatin tarayya 74, da na jihohi ko kananan hukumomin da ke amfani da malaman jinya a fadin kasar.
NANNM na bukatar aiwatar da tsarin albashi, karin kayan aiki, daukar ma’aikata, da kuma dakatar da rage kudin alawus ga malaman jinya.
Asali: Legit.ng