'Dan Najeriya Ya Fitar da Fassarar Kur'ani Irinta Ta Farko a Duniya bayan Aikin Shekaru 22
- Dr Dauda Awwal ya ƙaddamar da Alƙur’ani na musamman da ke ɗauke da haruffan Larabci, fassarar Yarbanci da kuma na Turanci
- Rahotanni sun nuna cewa malamin ya ɗauki tsawon shekara 22 yana gudanar da wannan aiki mai wahala da muhimmanci
- Ya bayyana cewa za a raba fiye da guda miliyan 5 a nahiyoyi 4 na wannan Kur'ani, tare da ƙirƙirar tsarin yada shi a yanar gizo
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos – Wani malamin addinin Musulunci ɗan Najeriya, Dr Dauda Awwal, ya ƙaddamar da abin da ya bayyana a matsayin fassarar Alƙur’ani ta farko a duniya.
Malamin ya ce ya haɗa harshen Yarbanci da Turanci, tare da haruffan Larabci da na Romawa, domin sauƙaƙa fahimtar Alƙur’ani ga al’ummar Yarbawa a duk faɗin duniya.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da malamin ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafin shi na Facebook a watan da ya wuce.
Malamin ya ce littafin mai suna Global English-Yoruba Qur’an 4-in-1 ya ƙunshi:
- Rubutun Larabci na asali
- Rubutu da haruffan Romawa
- Fassarar Yarbanci
- Fassarar Turanci da aka ƙawata da sharhi, hadisai da bayanan kimiyya
“A karo na farko a tarihi, an haɗa waɗannan abubuwa huɗu a cikin Alƙur’ani guda,”
- Inji Dr Awwal, wanda ya kammala karatu daga jami’ar Muhammad Ibn Saud da ke Riyadh.
Za a rabawa yara Kur'anin
Dr Awwal ya kuma ƙaddamar da wani Kur'ani ga yara masu shekaru 5 zuwa 10, wanda ke ƙunshe da surori 13 tare da zane-zane da sauti domin yada ilimin addini tun daga ƙuruciya.
Punch ta wallafa cewa ya ce ana shirin raba bugu miliyan 5 kyauta a nahiyoyi huɗu: miliyan 2 a Afirka, miliyan 1 a Turai, Asiya da Amurka.
Kalubalen da malamin ya fuskanta
Rahotanni sun nuna cewa Dr Awwal ya ce wannan aiki da ya ɗauki shekara 22 yana yi ya fuskanci ƙalubale da dama a cikinsa.
“Na sadaukar da lokaci da kuɗi. Na yi nazarin daruruwan littattafai, na saye kayayyaki da yawa da tsada, na je kasashe daban-daban don neman ingantattun bayanai,”
In ji shi.
Manufar fassarar Kur'anin da roƙon tallafi
Dr Awwal ya bayyana cewa manufarsa ita ce cike gibin rashin cikakkiyar fassarar Alƙur’ani ga Yarbawa.
Ya buƙaci taimako daga ƙasashen Musulmi da masu hannu da shuni, ciki har da Yariman Saudiyya, domin yada aikin a matakin duniya.

Source: UGC
Malamin musulunci ya rasu a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa Allah ya karbi rayuwar wani malamin addinin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Shua'ibu A. Ahmad.
Rahotanni sun nuna cewa malamin ya sha fama da doguwar rashin lafiya kafin Allah ya karbi rayuwar shi.
Bayanan da Legit ta samu sun nuna cewa marigayin ne shugaban majalisar malaman Izala a unguwar Jekadafari Kudu da ke Gombe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

