Allah ya yi wa sananniyar mai fassara Al-Qur'ani mai girma rasuwa

Allah ya yi wa sananniyar mai fassara Al-Qur'ani mai girma rasuwa

- Valeria (Iman) Porkhova, sananniyar mai fassara Al-Qur'ani da yaren Rasha ta rasu

- Ta rasu ne tana da shekaru 79 a duniya

- Fassararta kadai ce wacce aka yi da ayoyi kuma manyan malaman musulunci na duniya suka aminta da ita

Sananniyar mai fassara Al-Qur'ani da yaren Rasha, Valeria (Iman) Porkhova, ta rasu a Moscow tana da shekaru 79 a duniya.

Kafafen yada labarai na Rasha sun ruwaito cewa ta rasu ne a ranar Litinin, 2 ga watan Satumba. Rahoton ya kara da cewa addu'ar tunawa da ita a ranar Laraba 4 ga watan Satumba a wani masallaci da ke Moscow.

An haifeta a shekarar 1949 a garin Tsarskoye Selo a kasar Rasha. Porokhova ta kammala karatunta a Moscow State Pedagogical Institute of Foreign Languages kuma tayi aikin koyarwa na shekaru 18. Daga baya ta koma aiki a Russian Academy of Natural Sciences.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya bayyana dalilan da suka hana yin taron majalisar zartarwa a yau

A shekarar 1975, ta auri wani dan kasar Syria inda suka bar Moscow zuwa Damascus a 1981 inda ta amshi musulunci ta kuma sami sunanta na Iman.

A kasar Syria ta fara aikin fassara Al-Qur'ani mai girma zuwa yaren kasar Rasha. Ta kammala fassarar a 1991.

Rahoto ya nuna cewa fassararta ita kadai ce wacce aka yi da ayoyi kuma malaman musulunci na kasashe daban-daban da suka hada da jamhuriyar Soviet suka aminta da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel