Kaduna: Uba Sani Ya Warware Zargin Musayar Kuɗi tsakanin Gwamnatinsa da Ƴan Ta'adda

Kaduna: Uba Sani Ya Warware Zargin Musayar Kuɗi tsakanin Gwamnatinsa da Ƴan Ta'adda

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi martani ga masu zargin gwamnatinsa da biyan kudin fansa ga 'yan bindiga
  • Ya ce tun bayan da ya hau mulki wasu ke zargin yana sakar wa ƴan ta'adda kuɗi domin a samu zaman lafiya a Kaduna
  • Gwamnan ya ce babu ƙamshin gaskiya a zargin, kuma a matsayinsa na mai son jama'arsa, na zai biye wa ƴan ta'adda ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Gwamnatin jihar Kaduna ta yi martani a kan zargin da aka daɗe ana yi cewar tana biyan ƴan ta'adda kuɗin fansa.

Gwamnan jihar, Uba Sani, ya ƙaryata zargin da ake yi masa na biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda domin su riƙa sakin mutanen da su ke yi wa ɗauki ɗai-ɗai.

Kara karanta wannan

ADC ta yi bayani kan rashin sauya sheƙar El Rufa'i da Obi har yanzu

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani
Uba Sani ya yi magana kan biyan fansa Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

A wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na tashar Arise Television a ranar Alhamis, gwamnan ya ce bai taba biyan ko sisin kwabo ga ‘yan bindiga ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani ya musanta biyan fansa a Kaduna

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Uba Sani ya tuna cewa lokacin da ya hau kujerar mulki, akwai masu zargin shi da kokarin sulhu ta hanyar biyan kudi ga ‘yan bindiga domin magance matsalar rashin tsaro a jihar.

A cewarsa:

“Na fada masu cewa mutum kamar ni, wanda ya tsaya wajen kare hakkin talakawa da ‘yan kasa ba zai zauna da ‘yan bindiga ba.”

Gwamnan ya ce makonni biyu da suka wuce ya kaddamar da wani shiri na gina gidaje ga wadanda suka rasa matsuguni sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda.

Ya ce:

“Ban taba biyan ko Naira daya ba ga ‘yan bindiga, amma na gina gidaje ga wadanda suka sha wahala a Kaduna.”

Kara karanta wannan

ADC: 'Yadda gwamnoni da hadimai ke cika kunnen Tinubu da karya da gaskiya'

Uba Sani ya magantu kan taimakon jama'a

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa irin wannan tallafa wa al'umma na bukatar hadin gwiwar jama'a domin cimma nasara.

Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna
Uba Sani ya musanta zargin biyan kuɗin fansa Hoton: Senator Uba Sani
Source: Twitter

Ya ce:

“Gwamna kadai ba zai iya jagorantar hakan ba; sai an samu goyon bayan al'umma."

A gefe guda kuma gwamnan ya ce babu wani rikici tsakanin manoma da makiyaya da aka samu a jihar Kaduna kwanan nan saboda salon mulkinsa.

A cewarsa:

“A yau a jihar Kaduna, ba mu samu ko da rikici daya ba tsakanin manoma da makiyaya. Mun warware matsalar ne ta hanyar hadin kai. Dole ne a hada kai. Shugaba Tinubu bai da bukatar zuwa arewa don ya koya maka yadda za ka tafiyar da jiharka.”
“A yau a jihar Kaduna, ba mu samu ko da rikici daya ba tsakanin manoma da makiyaya. Mun warware matsalar ne ta hanyar hadin kai. Dole ne a hada kai.

Gwamnati za ta samar da aiki a Kaduna

Kara karanta wannan

"Lokaci ya yi" Gwamnatin Tinubu ta yiwa ƴan bindiga 'tayi' a Arewacin Najeriya

A baya, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana aniyar ta na farfado da tsohon kamfanin sarrafa auduga da ke jihar Kaduna domin farfaɗo da tattalin arziƙi.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa kan nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Akume ya bayyana cewa hakan na cikin muhimman tsare-tsare da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa domin tabbatar da daidaito da cigaba mai dorewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng