'Su Ƙona Gidajenmu, Su Harbe Mu:' Yadda Ƴan Bindiga Su ka Dawo Katsina da Ƙarfinsu
- Fiye da mutane 5,000 sun tsere daga hare-haren ‘yan bindiga a jihar Katsina, suna neman mafaka a makwabtan ƙauyukansu
- Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka ƴan bindiga sun dawo da cin karensu babu babbaka a wasu ƙauyukan Katsina
- Ƙauyukan da al'amarin ya fi muni sun haɗa da Anguwar Galadima, Gidan Sule, Gidan Chiwake, Gidan Dan Maye da Gidan Gagare
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Akalla mutane 5,000 da suka tsere daga hare-haren ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin Bakori da Faskari a jihar Katsina sun koma garin Bakori.
Rahotanni daga yankin sun tabbatar da cewa fiye da kauyuka 10 da suka hada da Guga, Anguwar Danmarka, sun shiga cikin masifar dawowar hare-haren ƴan bindiga.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta dukufa a kan ilimi, ta gyara fiye da makarantu 1,200 a sassan jihar

Source: Facebook
Wani rahoto da ya keɓanta ga Daily Trust ya ce sauran ƙauyukan da su ka shiga halin ni ƴa su akwai Anguwar Galadima, Gidan Sule, Gidan Chiwake, Gidan Dan Maye, Gidan Gagare, Gidan Sarkin Noma da Gidan Nakuba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jama'a na cikin fargaba a Katsina
Rahotanni sun tabbatar da cewa ko da yake jami’an tsaro da ‘yan banga na ci gaba da kokarin dakile hare-haren, har yanzu ana fuskantar matsin lamba daga ‘yan bindiga.
An gano miyagun mutanen na ci gaba da kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma satar shanu yayin da suke barazana ga zaman lafiya a Katsina.

Source: Twitter
A wani sabon hari da aka kai a safiyar Laraba, an sace mutum biyar a karamar hukumar Dutsinma, ciki har da wani attajiri mai suna Alhaji Babangida Maigoro.
“Sun ƙona gidajenmu da rumbunan abinci," Mazauna Katsina
Wani dattijo mai shekara 68 daga kauyen Doma, Yusuf Usman, ya bayyana cewa fiye da mutum 250 aka kashe a kauyensu da kewaye tun shekarun baya.
“Sun kashe iyalanmu, sun ƙona mana rumbuna da gidaje, sannan suna tafiya da mu daji, daga ciki har da mata da yara kamar dabbobi."
Wata mata mai suna Murja Sufyan daga Anguwar Galadima ta ce tana zaune a Bakori tsawon kusan wata biyu saboda harin da ya tilasta musu yin hijira.
“Mutane fiye da 20 aka sace daga kauyenmu. Daga cikin iyalina 17, mun tsere saboda hare-haren ba su da lokaci — ko rana ko dare za su iya zuwa."
Yayin da fiye da mutum 5,000 suka nemi mafaka a makwabtan ƙauyuka, da yawa daga cikinsu na zaune a cikin mawuyacin hali mai cike da tausayi.
An kashe jami'an tsaro a jihar Kastina
A baya kun ji gwamnatin Katsina ta bayyana cewa dakarun jami’an tsaro fiye da 130 ne suka rasu a yaƙi da ta'addanci daga shekarar 2023 zuwa yau a jihar.
Gwamnatin ta ce daga cikin waɗanda su ka rasu a bakin aiki har da jami'an tsaron sa-kai na Community Watch Corps, sojoji da ‘yan sanda.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida na jihar, Dr. Nasir Mu’azu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar domin karyata rahotannin lalacewar tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
