ADC: 'Yadda Gwamnoni da Hadimai ke Cika Kunnen Tinubu da Karya da Gaskiya'
- Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa sam, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai san halin da ƙasa ke ciki ba
- Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na riƙo, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan, tare da sukar hadiman Tinubu
- Ya zarge su da sharara masa ƙarya don su burge shi, amma ba a sanar da shi wahalar da talaka ke sha
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Bolaji Abdullahi, muƙaddashin Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ADC, ya zargi shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin sanin ainihin halin da Najeriya ke ciki.
Ya bayyana cewa kamata ya yi Shugaba Tinubu ya daina dogaro da rahotannin da hadimansa ke ba shi, ya fita kai tsaye ya ji daga bakin 'yan ƙasa don fahimtar halin da ake ciki.

Source: Facebook
Abdullahi ya bayyana haka ne a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Laraba, inda ya soki hadimin shugaban ƙasa, Daniel Bwala, saboda rage girman matsalar tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ADC ta caccaki hadimin Bola Tinubu
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Abdullahi ya bayyana cewa shugaban ƙasa Tinubu yana zaune ne cikin duhu.
Ya ce:
“Ina jin tausayin shugaban ƙasa Tinubu saboda idan wannan ne irin labaran da yake samu kullum, to hakan na nuna cewa yana rayuwa ne cikin duniyar da ba ta da alaƙa da gaskiyar halin da ake ciki.”
Ya ƙara da cewa Bwala yana ƙoƙarin nuna Najeriya tamkar aljanna ce, alhali kuwa akasin haka ne ke faruwa.

Source: Facebook
Abdullahi ya bada misalin sace ɗaliban dalibai lauyoyi guda shida da aka nemi fansar Naira miliyan 120 a kansu, yana mai cewa wannan lamari na nuna yadda matsalar tsaro ke ƙara kamari ba raguwa ba.
ADC ta ce akwai rashin tsaro a ƙasa
Jam’iyyar adawa ta ADC ta nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ci gaba da addabar ƙasa, duk da ikirarin da gwamnatin Tinubu ke yi cewa an samu sauƙi.
Abdullahi ya ce:
“Bwala na cewa an rage matsalar tsaro, alhali akwai ɗaliban lauyoyi guda shida da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane.”
"Ina ganin ya kamata shugaban ƙasa Tinubu ya bar fadar gwamnati, ya fita ya zaga gari, ya ji da kunnensa daga bakin mutane, maimakon dogara da irin wannan labari.”
“Haka kuma, ya daina sauraron gwamnoni da ke kokarin nuna masa abin da zai burge shi ne kawai, ba gaskiyar da mutane ke ciki ba.”
Jagora a Jam'iyyar ADC ya yi fallasa
A baya, kun samu labarin cewa tsohon shugaban jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya bayyana cewa jam'iyya mai mulki ta APC ta so ta yi katsalandan a haɗakar adawa.
Mista Nwosu ya ce wasu jami’an gwamnatin Bola Ahmed Tinubu sun nemi ya janye daga shirin hadakar jam’iyyun adawa tare da yi masa tayin kujerun ministoci.
A cewar Nwosu, an ce zai karɓi kujerar minista guda ɗaya, sannan ya ba wanda ya ga dama sauran biyu duk don kada ya miƙa ADC ga haɗakar ƴan adawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

