Hadimin Tinubu Ya Fito da Bayanin Irin Kuɗin da Gwamnonin Jihohi ke Samu a Yau
- Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa babu wani gwamna da ke cikin ƙunci wajen biyan albashi a ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu
- Hadimin shugaban ƙasa, Nista Daniel Bwala ne ya bayyana haka, inda ya ce gwamnatin tarayya ta buɗe bakin lalitarta ga gwamnoni
- Ya ce babu wani gwamna da zai iya bugar ƙirji ya ce yana fama da rashin kuɗi, saboda ana samun alheri kamar a lokacin farkon gano man fetur
FCT, Abuja – Daniel Bwala, mai ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan sadarwa ya faɗi halin da gwamnonin Najeriya ke ciki.
Bwala ya bayyana cewa gwamnonin ƙasar nan na cin moriyar gagarumin ci gaba tattalin arziƙi da kuɗi daga asusun gwamnatin tarayya.

Source: Facebook
Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Laraba.
Ya ƙara da bayyana cewa a yanzu haka, babu wani gwamna da ke cikin halin ƙunci da rashin kuɗi ya jawo.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya cika alkawarin samar da tsaro a Najeriya, an kafa hujja da jihohi 2
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daniel Bwala: 'Gwamnonin Jihohi na more wa'
Jaridar The Cable, ta ruwaito Bwala ya ce ba kamar yadda aka sha fama a baya ba inda wasu gwamnonin ke shan wahala wajen biyan albashi, yanzu haka dukkanninsu na cikin alheri.
Ya ce:
“Dukkannin gwamnonin Najeriya na cikin alheri , kuma suna cikin yanayi mafi kyau a tarihin gwamnatocinsu, kamar yadda aka ce an samu wadata a farkon gano man fetur.”
“Jihohi 27 sun taba kasancewa cikin yanayin mara daɗi na durƙushewar tattalin arziki, inda ba a biyan albashi. Amma yanzu ba wannan ake maganar ake ba.”
“Yanzu dai kusan laifi ne ko saɓo mutum ya ce ba a biyan albashi."
An samu karin kudin shiga,' Inji Bwala
Daniel Bwala ya ƙara da cewa gwamnatin yanzu na samun kuɗin shiga da ya isa biyan albashi, gudanar da ayyuka, da aiwatar da sauran aikace-aikace.
Ya ce:
“Akwai kuɗin shiga da za su isa a biya mafi ƙarancin albashi, su aiwatar da ayyuka, su biya bashi, har ma su yi tanadi don gaba.”

Source: Twitter
Wannan furuci na Bwala ya biyo bayan kalaman Gwamna Uba Sani na Kaduna, wanda ya bayyana cewa yana da wuya wani gwamna ya iya adawa da sake tsayawar Tinubu a zaɓen 2027.
A cewarsa:
“Babu wani shugaban ƙasa a tarihin Najeriya da ya bai wa gwamnonin jihohi da gwamnatocin ƙananan hukumomi goyon baya kamar yadda Bola Ahmed Tinubu ke yi yanzu.”
“Saboda haka, yana da matuƙar wahala a ce wani gwamna zai yi adawa da shi."
Hadimin Tinubu ya caccaki jagoran ADC
A baya, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta yi watsi da zargin da tsohon shugaban jam’iyyar ADC, Mista Ralph Nwosu ya yi a kan wasu manyan jami'an gwamnati.
Ralph Nwosu ya yi zargin cewa wasu manyan jami’an gwamnatin Bola Ahmed Tinubu sun yi masa alkawarin kujerun ministoci guda uku don ya taɗe yunƙurin ƴan adawa
Sai dai Daniel Bwala ya ce duk wata muhimmiyar magana ta siyasa irin wannan, dole ta fito daga bakin shugaban ƙasa kai tsaye ba muƙarraban gwamnati ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
