Kwana 1 da Ziyarar Matar Tinubu, Gwamna Alia Ya Kori Dukkan Kwamishinoni daga Aiki

Kwana 1 da Ziyarar Matar Tinubu, Gwamna Alia Ya Kori Dukkan Kwamishinoni daga Aiki

  • Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya kori dukkanin kwamishinoninsa daga majalisar zartarwa tare da naɗa shugaban ma’aikata
  • Barista Moses Atagher da ya taba rike kwamishinan shari’a da kuma shugaban bankin FMB, ya zama sabon shugaban ma’aikatan
  • Gwamna Alia ya sanar da korar kwamishinonin da naɗa Atagher a ƙarshen taron majalisar zartarwar jihar karo na 12 a birnin Makurdi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - A wani mataki da ya ba kowa mamaki, gwamnan Benue, Hyacinth Alia ya sanar da rushe majalisar zartarwar jihar.

A yammacin ranar Laraba, Mai Girma Hyacinth Alia ya kori dukkanin kwamishinonin daga aiki, tare da naɗa muƙami ɗaya kacal.

Gwamnan Benue, Hyacinth Alia ya sanar da korar dukkanin kwamishinonin jihar
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya halarci taron kungiyar gwamnoni (NGF). Hoto: @HyacinthAlia
Source: Twitter

Gwamnan Ali ya nada shugaban ma'aikata

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamnan ya naɗa shugaban ma'aikatan gidan gwamnati (CoS) bayan sallamar kwamishinonin.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta ɗauki zafi kan zargin yiwa ƙusa a ADC tayin kujerun ministoci

Hyacinth Alia ya amince da naɗin Barista Moses Atagher, wanda ya riƙe kujerar babban lauyan jiha kuma kwamishinan shari'a har sau biyu a matsayin shugaban ma'aikatan.

Kafin zama shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Benue, Barista Atagher ya taba rike shugabancin bankin lamunin gidaje na tarayya (FMB).

Sanarwar mai magana da yawun gwamnan, Tersoo Kula, ta nuna cewa Barista Atagher zai kama aiki ne nan take, ba tare da ɓata lokaci ba.

Gwamna Alia ya kori dukkanin kwamishinoni

Tersoo Kula ya kuma sanar da cewa Gwamna Alia ya sanya hannu kan korar kwamishinonin da naɗa sabon shugaban ma'aikatan ne a ƙarshen taron majalisar zartarwa na jihar Benue karo na 12 (2025).

"Gwamnan ya yaba da irin kokarin da kowanne kwamishina ya nuna tsawon shekara biyu da suka yi aiki a majalisar zartarwar jihar.
"Ya kuma roƙi waɗanda ba za a sabunta naɗinsu ba da ka da su yi fushi, su ci gaba da zama a cikin jam'iyyar don ba da shawarwari.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Uba Sani ya yi murabus, an maye gurbinsa da sabo

"Gwamnan ya ce zaman tsofaffin kwamishinonin a jam'iyyar ne zai sa sababbin kwamishinonin da za a naɗa su yi saurin fahimtar ayyukansu."

- Tersoo Kula.

Gwamna Hyacinth Alia ya naɗa sabon shugaban ma'aikatan gidan gwamnati
Gwamnan jihar Benue Hyacinth Alia yana jawabi a wani taro. Hoto: @HyacinthAlia
Source: Twitter

Kwamishinonin da aka kora sun yi magana

Channels TV ta rahoto Tersoo Kula ya ƙara da cewa idan aka cire shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, wannan sallamar ta shafi iya kwamishinonin jihar ne kawai.

Da ya ke jawabi a madadin kwamishinonin da aka kora, Barista Bemsen Mnyim, a cewar sanarwar, ya godewa gwamnan kan damar da aka ba su ta yiwa jihar hidima.

An ruwaito Barista Mnyim yana cewa:

"A kowace irin gaba ta rayuwa, duk inda aka kira ka aka ce ka yiwa jama'a hidima, to ka dauka za ka je makaranta ne. Mun koyi abubuwa da yawa a yayin aiki da kai."

A hannu ɗaya kuma, an umarci tsofaffin kwamishinonin da su miƙa ragamar ayyukansu ga manyan sakatarorin hukumominsu ba tare da ɓata lokaci ba.

Matar Tinubu ta raba N1bn a Benue

A wani labarin, mun ruwaito cewa uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta kai ziyarar jaje zuwa jihar Benue.

Kara karanta wannan

SDP ta fice daga haɗakarsu Atiku, za ta fito da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027

Yayin da take jajantawa jihar kan hare-haren ƴan bindiga, Remi Tinubu ta ba ƴan gudun hijira tallafin N1bn.

Jim kadan da tafiyarta, ƴan gudun hijira sun barke da zanga-zanga, suna zargin gwamnatin jihar da hana su kuɗin tallafi da ake ba su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com