'A Taimaka Masa kamar Buhari': An Roƙawa Tinubu Alfarma Wurin Ƴan Arewa a 2027
- Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Bola Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu kamar marigayi Muhammadu Buhari
- Onanuga ya karyata zargin nuna wariya, yana cewa ana kokarin rage karfin Tinubu saboda asalin sa dan Kudu ne
- Ya ce mukamai masu muhimmanci a harkar tsaro suna hannun ‘yan Arewa, kuma tsaro ya inganta a wurare irin su Birnin Gwari da Igabi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa, Bola Tinubu shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya roki yan Arewa alfarma.
Onanuga ya ce Tinubu ya cancanci neman wa’adi na biyu kamar yadda Muhammadu Buhari ya yi kafin rasuwarsa.

Source: Twitter
2027: Hadimin Tinubu ya roki yan Arewa
Yayin wata hira da yan jarida a ranar Laraba, Onanuga ya yi watsi da zargin wariya daga kungiyar ACF, cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onanuga ya bukaci ’yan siyasar Arewa da su yi hakuri, su bar Kudu ta kammala wa'adinta na mulki, yana mai cewa Kudu ma ta yi hakuri lokacin mulkin Buhari.
Hadimin shugaban ƙasa ya ce hakan wani salo ne na sukar gwamnatin Tinubu da dabarun hana Kudu karisa wa'adinsu.
Onanuga ya gano makircin sukar Tinubu a Arewa
Ya ce sukar da ake yi wa Tinubu wani yunkuri ne da ake yi don rage darajarsa saboda ya fito daga Kudu, ba don wani dalili na gaskiya ba.
Ya ce:
“Wannan shugaban kasa dan Najeriya ne, ya cancanci wa’adi biyu kamar yadda Buhari ya samu, ka da mu sadaukar da kasa saboda son rai."

Source: Facebook
Onanuga ya ƙaryata zargin fifita Kudu kan Arewa
Game da zargin fifita yankin Kudu maso Yamma wajen nade-naden gwamnati, Onanuga ya kalubalanci masu zargi da su kawo hujja ta lissafi, ba kalmomi kawai ba.

Kara karanta wannan
'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'
Ya kuma ce ba gaskiya ba ne cewa an yi watsi da ayyukan Arewa, domin gwamnatin Tinubu ta gaji manyan ayyukan da aka bari babu kammalawa.
Onanuga ya kawo hujja da mukaman tsaro da ’yan Arewa ke rike da su, yana mai cewa hakan na nuna adalci a nade-naden gwamnatin Tinubu.
“Kuna bukatar daidaitattun kididdiga. Wannan siyasa ce kawai don rage karfin shugaban kasa. Akwai tituna marasa kyau a ko’ina, ba Arewa kadai ba.
“Mai Ba da Shawara kan Tsaro, Shugaban Rundunar Soji, da Ministocin Tsaro duka ’yan Arewa ne. Birnin Gwari da Igabi sun fi samun zaman lafiya yanzu.
"Na bi hanyar Kaduna zuwa Abuja ba tare da hadari ba, wanda a da ba zai yiwu ba.”
- Bayo Onanuga
Minista ya ce Tinubu ya cika alkawuransa a Arewa
Mun ba ku labarin cewa ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya tabo batun alkawuran da Bola Ahmed Tinubu ya yi wa yankin Arewa.
Mohammed Idris ya bayyana cewa yankin Arewa bai bin Shugaba Tinubu bashi kan alkawuran da ya dauka kafin zaben 2023.
Ministan nuna cewa shugaban kasan ya saka 'yan Arewa masu yawa a cikin gwamnatinsa domin yin aiki tare da shi, akasin zargin wasu mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
