NiMet: Za a Sha Ruwan Sama da Tsawa a Yobe, Katsina da Jihohi 27 a Ranar Alhamis
- Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama hade da tsawa a wasu jihohin Arewa ciki har da Borno, Yobe da Katsina
- Jihohin Kudancin Najeriya kamar Enugu, Ebonyi da Cross River suma za su samu ruwan sama mai dan karfi daga yamma zuwa dare
- NiMet ta ja hankalin jama'a da su guji fakewa a karkashin bishiyoyi da kuma yin tuƙi a lokacin ruwan sama domin gujewa haɗurra
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar kula da hasashen tanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen saukar ruwa da ambaliya na ranar Alhamis, 31 ga Yulin 2025.
A gobe Alhamis, idan Allah ya kaimu, NiMet ta ce za a iya samun samun saukar ruwan sama hade da tsawa a jihohi daban-daban na ƙasar nan.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Dakarun Sojoji sun hallaka ƴan bindiga sama da 3,000 a jihohin Arewa

Source: Getty Images
Hasashen yanayin na ranar Alhamis na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NiMet ta fitar a daren ranar Laraba, 30 ga Yulin 2025 a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hasashen yanayi a jihohin Arewa
Sanarwar NiMet ta ce:
"Ana sa ran ruwan sama zai sauka hade da tsawa a sassan jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Zamfara, Kebbi, Kaduna, Taraba, Bauchi, da Katsina.
"Da yammaci har zuwa dare kuwa, hasashen yanayin ya nuna cewa za a sha ruwan sama mai matsakaicin karfi a faɗin yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas."
Da safiyar Alhamis din, NiMet ta ce akwai yiwuwar a samu yayyafi zuwa ruwa mai matsakaicin ƙarfi a sassan babban birnin tarayya da jihohin Neja da Nasarawa.
"Sannan za a iya samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi zuwa mai ƙarfi a sassan babban birnin tarayya da jihohin Nasarawa, Kwara, Kogi, Plateau, Neja da Benuwe da yamma zuwa dare."

Kara karanta wannan
Hotuna: An ga yadda ambaliyar ruwa ta rusa gidaje a Borno, mutane sun fara hijira
- NIMET
Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya
Hasashen yanayin NiMet na ranar Alhamis bai tsaya iya kan jihohin Arewa ba, domin ko a Kudancin Najeriya, hukumar ta yi hasashen cewa:
"Za a samu hadari tare da yiwuwar saukar ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Enugu, Ebonyi, da Cross River.
"Amma ana sa ran ruwan sama mai dan ƙarfi a sassan jihohin Ekiti, Oyo, Ondo, Abia, Imo, Ebonyi, Enugu, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River, da Akwa Ibom daga yamma zuwa dare."

Source: Original
Hukumar NiMet ta gargadi jama'a
NiMet ta shawarci jama'a da su ɗauki matakan da suka dace game da iska mai ƙarfi, walƙiya, da ambaliyar ruwa, musamman a lokacin ruwan sama mai karfi.
Har ila yau, hukumar ta ce akwai bukatar direbobi su guji tuƙi a lokacin ruwan sama mai ƙarfi don kaucewa haɗari, kuma a guji neman mafaka a ƙarƙashin bishiyoyi yayin don gudun karyewar rassan bishiyoyin.
Ga filayen sauka da tashin jiragen sama da ma kamfanin jiragen sama, NiMet ta bukaci su nemi bayanan yanayi daga gareta don tsara tafiye-tafiyen jirage.
Ambaliya ta rusa gidaje a Maiduguri
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mamako ruwan sama da aka zabga na akalla awanni uku ya haddasa ambaliya a wasu sassan Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Rundunar 'yan sanda a jihar Borno ta sanar da cewa ruwan saman da aka yi ya jawo gine-gine takwas sun rushe yayin da mutane suka fara barin gidajensu.
Rundunar ta kuma bayyana cewa ta tura tawa domin ceto wadanda suka makale tare da ba da kariya ga gidaje da dukiyoyinsu don gudun kada barayi su sace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
