Abin da DSS Suka Yi Wa Ɗan TikTok da Ake Zargin Ya Ce Tinubu Ya Mutu sanadin Guba

Abin da DSS Suka Yi Wa Ɗan TikTok da Ake Zargin Ya Ce Tinubu Ya Mutu sanadin Guba

  • Lauya Hamza Nuhu Dantani ya bayyana yadda jami'an DSS suka durfafi gidan yarin da aka garkame dan TikTok
  • Dantani ya ce jami’an DSS sun tilasta wa dan TikTok, Ghali Ismail fadin bayanan sirri na wayarsa da asusun imel dinsa
  • Ismail, wanda ake kira Sultan, yana gidan gyaran hali na Keffi bayan kotu ta bayar da umarnin tsare shi kan yada bidiyon rashin lafiyar Bola Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Keffi, Nasarawa - Lauya kuma mai kare hakkin bil’adama, Hamza Nuhu Dantani ya zargi DSS da take hakkin dan Adam.

Hamza Dantani ya bayyana damuwa kan tilasta wa wani dan TikTok, Ghali Ismail, bayar da bayanan sirri na wayarsa.

DSS sun ci zarafin dan TikTok, Sultan
DSS sun kwace bayanan sirri na wayoyin dan TikTok, Sultan. Hoto: Hamza Nuhu Dantani.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani rubutu a Facebook ranar Laraba, Hamza Dantani ya ce ba su san dalilin sababbin matakan DSS ba a halin yanzu.

Kara karanta wannan

'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da wani laifin ake zargin Sultan?

Legit Hausa ta ruwaito cewa wata kotun majistare da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Ismail a gidan gyaran hali na Keffi ranar Jumma’a.

An kama dan TikTok ɗin da aka fi sani da Sultan, bayan zargin fitar da bidiyo a shafinsa yana cewa Bola Tinubu ya mutu.

A cikin bidiyon, ya ce an ba Tinubu guba ne da gangan har ya mutu saboda wata matsala da ya samu bayan guba ta kama shi.

Bayan haka, jami’an DSS sun gurfanar da shi a kotu kan tuhume-tuhume biyu: watsa ƙarya da kuma tunzura jama’a kan gwamnati.

Zargin lauya kan jami'an hukumar DSS

Wannan lamari ya janyo suka mai tsanani daga jama’a da masu rajin kare hakkin dan Adam a kan gwamnatin tarayya.

A cikin rubutunsa, Dantani ya ce:

Ya ce:

“Jiya da dare, jami’an SSS sun je gidan gyaran hali na Keffi, suka tilasta wa Sultan bayar da bayanan sirrin wayoyinsa da imel.

Kara karanta wannan

Hotuna: An ga yadda ambaliyar ruwa ta rusa gidaje a Borno, mutane sun fara hijira

“Yanzu haka, ba mu san manufarsu ba kan wannan karya dokar da suka aikata.
“Wannan abu ya sabawa doka, bai dace ba, kuma ya ci karo da tsarin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ana zargin DSS da take hakkin dan TikTok
DSS sun kwace bayanan sirri na dan TikTok a gidan yari. Hoto: UGC.
Source: Facebook

Lauya ya kalubalanci abin da DSS tayi

Dantani ya bayyana cewa ba su da ikon yin haka domin tun bayan gurfanar da shi a kotu da kai shi gidan yari ya nuna bincikensu ya kammala.

Ya kara da cewa:

“A lokacin da suka gurfanar da shi a kotu, ya nuna cewa bincikensu ya kammala, don haka ba su da ikon ci gaba da hakan.
“Doka ta tanadi cewa kafin jami’an tsaro su je masa a gidan yari, sai da umarnin kotu da kuma sanar da lauyoyinsa.
“Mun sanar da hukumar SSS wannan mataki marar kyau, kuma zan bi mataki na shigar da ƙara a hukumance.

An zargi matar sanata da cin zarafin matashi

Kun ji cewa yan Najeriya da dama sun soki matar sanata a jihar Taraba kan cafke matashi da kuma cin zarafinsa na tsawon kwanaki.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan barkewar rikicin kabilanci a Abuja, an tafka barna

Matar Sanata Shuaibu Isa Lau ta umarci a kama wani matashi mai suna Nafiu Hassan kan wallafa bidiyo kan halin da yankin Lau ke ciki.

Nafiu ya fadawa Legit Hausa yadda abin ya faru bayan fitar da wasu faifan bidiyo guda uku da ke da alaka da mazabar sanata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.