Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan ISWAP, An Tura Miyagu Barzahu

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan ISWAP, An Tura Miyagu Barzahu

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi artabu da 'yan ta'addan kungiyar ISWAP wadanda ke tayar da kayar baya a jihar Borno
  • Sojojin na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda guda biyu bayan sun yi musayar wuta mai zafi
  • Hakazalika, jami'an tsaron sun kwato makamai masu yawa a artabun da suka yi da 'yan ta'addan a kauyen Aligambari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya a ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai sun kashe wasu ‘yan ta’adda biyu da ake zargin ‘yan kungiyar ISWAP ne a Borno.

Dakarun sojojin sun hallaka 'yan ta'addan na ISWAP ne a wani aikin sintiri da suka gudanar a ƙauyen Aligambari, kusa da Gajiram, cikin jihar Borno.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP
Sojojin sun kashe 'yan ta'addan ISWAP a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Dakarun Sojoji sun hallaka ƴan bindiga sama da 3,000 a jihohin Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa dakarun, bisa sahihan bayanan sirri da suka samu, sun ƙaddamar da wani samame a yankin ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Litinin.

A cewarsa, dakarun sun haɗu da ‘yan ta’addan a lokacin da suke sintiri, inda aka yi musayar wuta mai tsanani.

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan ISWAP

Sojojin sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu a yayin artabun da suka yi da masu tayar da kayar baya.

Bayan artabun, an kwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, bindiga kirar PKT, babbar bindiga mai jigida guda ɗaya da kuma gidan harsasai guda biyu daga hannun ‘yan ta’addan da aka kashe.

"Sojojin na ci gaba da mamaye yankin da ke ƙarƙashin kulawarsu tare da gudanar da sintiri mai zafi domin hana ‘yan ta’adda samun damammakin motsawa da kai hari."

- Wata majiya

Majiyar ta ƙara da cewa dukkan kayan da aka kama a hannun ‘yan ta’addan na hannun sojoji kuma ana jiran umarni daga mahukunta a sama don daukar mataki na gaba.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ritsa 'yan ta'addan Boko Haram a daji, an kashe miyagu

Rundunar Operation Hadin Kai dai na cigaba da nuna ƙarfin gwiwa da sadaukarwa wajen kawar da barazanar tsaro da ‘yan ta’adda ke haddasawa a yankin Arewa maso Gabas.

Wannan aiki da dakarun suka gudanar na daga cikin jerin nasarorin da ake samu a kokarin da gwamnati ke yi don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan ISWAP
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP a Borno Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan sojoji

Sojojin sama sun hallaka kwamandojin ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na Najeriya sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno.

Sojojin sun hallaka 'yan ta'addan ne bayan sun kai musu hare-hare a maboyarsu da ke cikin daji.

Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka kwamandojin ISWAP tare da mayaka masu yawa sakamakon hare-haren da suka kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng