'Yadda Tinubu Ya Ɗauko Gagarumin Aiki Tun na Zamanin Shagari saboda Ƙaunar Arewa'

'Yadda Tinubu Ya Ɗauko Gagarumin Aiki Tun na Zamanin Shagari saboda Ƙaunar Arewa'

  • Ministan tsare-tsaren kasafi kudi, Atiku Abubakar Bagudu ya bayyana irin yadda Bola Tinubu ke kaunar Arewa
  • Bagudu ya ce Tinubu na goyon bayan aikin titin Sokoto–Badagry duk da bai yi alkawarin hakan ba lokacin kamfe
  • Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu na mayar da hankali kan zuba jari a ababen more rayuwa don inganta tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Ministan tsare-tsaren kasafi da tattalin arziki, Atiku Bagudu ya yi magana game da soyayyar Bola Tinubu ga Arewa.

Bagudu ya ce Tinubu yana tallafa wa aikin titi daga Sokoto zuwa Badagry duk da cewa ba cikin alkawuran yakin neman zabensa bane.

Minista ta fadi fatan da Tinubu ya yi ga Arewa
Minista ya yabawa Tinubu kan ayyuka a Arewa. Hoto: Atiku Abubakar Bagudu.
Source: Twitter

Abin alherin da Tinubu ke yi a Arewa

Bagudu ya yi wannan bayani ne yayin zaman fasaha a taron tattaunawar gwamnati da jama’a wanda Gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

"Ya cika su": Minista ya yi bayani kan alkawuran da Tinubu ya yi wa Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin ministan ya biyo bayan zargin da Rabiu Kwankwaso, ya yi, inda ya ce gwamnatin tarayya na ware albarkatu da manyan ayyuka ga yanki daya kacal.

Sai dai Bagudu ya ce daya daga cikin manufofin gwamnati mai ci ita ce saka hannun jari a manyan ayyuka don tabbatar da ci gaba mai dorewa a fadin kasar.

Ya ambaci aikin titin Sokoto-Badagry wanda aka fara tsara tun zamanin jamhuriya ta uku a matsayin wani bangare na hangen nesa na tsohon Shugaba Shehu Shagari.

Ya ce:

"Shugaba Tinubu ya yi imani cewa sake gina Najeriya na bukatar muhimman ayyuka da ba lallai su shahara siyasance ba."
An yabawa Tinubu kan ayyukan alheri a Arewa
Atiku Bagudu ya ce har ayyukan da Tinubu bai yi alkawari ba yana yi a Arewa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Bagudu ya fadi kalubalen tattalin arziki

Bagudu ya bayyana cewa kalubalen tattalin arzikin Najeriya na yanzu na da nasaba da raunin tsarin da aka gada ciki har da matsalar musayar kudade da hauhawar bashi, The Nation ta tattaro.

"A lokacin da aka nada mu a matsayin ministoci, Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya ce mu dauki aikin kamar dibar ruwa daga rijiya busasshiya.

Kara karanta wannan

"Ƴan Arewa ba su yi nadama ba," Minista ya faɗi abin da ke faruwa a gwamnatin Tinubu

"Ya kamata mu fahimci cewa matsalar da muke ciki yanzu ta samo asali ne daga abubuwan da muka gada. Najeriya ta fuskanci koma bayan tattalin arziki biyu, fari da annobar korona."

- Atiku Bagudu

Ministan ya ce wahalhalun tattalin arzikin ne suka sa Tinubu ya kirkiro sabbin ma'aikatu da sauye-sauyen tsarin gwamnati guda takwas domin inganta mulki.

A cewarsa, ma’aikatun da aka kirkiro sun hada da tsare-tsaren kasafi da tattalin arziki, ci gaban dabbobi, fasaha da tattalin arzikin kirkira da bunkasa yankuna.

Ya kara da cewa:

“Gwamnati aiki ne mai ci gaba. Bayan da aka daidaita tattalin arziki, za a maida hankali wajen kara bunkasa ci gaba mai ma’ana da kawar da talauci."

Minista ya zayyano ayyukan Tinubu a Arewa

A wani labarin, ministan kasafin kudi, Atiku Bagudu ya bayyana cewa Arewa na da wakilci a gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Tinubu

Ministan ya ce ƴan Arewa ba su yi nadamar zaɓen Shugaba Tinubu ba domin yana mutunta wakilansu.

Ministan ya kuma musanta zargin nuna wariya da ake wa gwamnatin Tinubu, yana mai cewa da ƴan Arewa ake tafiyar da mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.