Hotuna: An ga yadda Ambaliyar Ruwa Ta Rusa Gidaje a Borno, Mutane Sun Fara Hijira
- Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliya a Maiduguri, inda mazauna wuraren da abin ya shafa suka fara hijira
- Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da afkuwar ambaliya a Bulumkutu da Gomari, har ta kai an tura jami’ai don ceto mutane kuma a hana sata
- Wannan ambaliya ta biyo bayan ruwan sama na tsawon sa’o’i uku, wanda ya jawo rushewar gine-gine takwas, a cewar 'yan sanda
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Mamakon ruwan sama a safiyar Laraba ya haddasa ambaliya da ta rushe gine-gine takwas tare da tilasta wa mutane tserewa daga gidajensu a Maiduguri, jihar Borno.
An tattaro cewa ruwan saman, wanda aka fara sheka shi da misalin ƙarfe 6:15 na safe, ya ɗauki kusan sa'o’i uku yana zuba.

Source: Twitter
Yadda ambaliya ta yi barna a Borno

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Dakarun Sojoji sun hallaka ƴan bindiga sama da 3,000 a jihohin Arewa
Jaridar Punch ta ce mamakon ruwan saman ne ya haifar da ambaliya a yankunan Bulumkutu, Abuja, Moduganari, Ngomari da wasu sassa na bakin kogi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu mazauna Bulumkutu, Ahmodu Ibrahim da Aisha Surajo, sun shaida wa manema labarai cewa ruwan ya yi masu gyara.
Ahmodu Ibrahim ya ce ruwan ya mamaye gidansa da misalin ƙarfe 8:00 na safe, wanda ya tilasta shi da iyalansa yin kaura.
"Na fara ganin ruwa yana shigowa bayan awa daya da fara ruwan saman. Nan take na fitar da matata da 'ya'yana zuwa wani wuri mafi aminci," inji Ahmodu .
Aisha Suraju, wata mai shago a yankin, ta ce kayan da take sayarwa da yawa sun lalace sanadiyyar ambaliyar.
“Ruwan da ya shiga shago na ya lalata kusan dukkanin kayan da nake ajiyewa a kasa, mun godewa Allah, amma ruwa ya yi gyara."
Matakin da 'yan sanda suka dauka a Borno
A wani bangare, rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta fara aikin ceton wadanda suka makale tare da tura jami’anta zuwa wuraren da ambaliyar ta shafa domin dakile duk wata barazana.
A cewar mai magana da yawun rundunar, ASP Nahum Daso, gidaje takwas ne suka rushe sakamakon mamakon ruwan saman.

Source: Twitter
Sanarwar ASP Daso ta ce:
“An samu afkuwar ambaliya sakamakon ruwan sama a yankunan Maiduguri, Gomari, Bulumkutu, Jidari, ITE da wasu yankuna.
"Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta gaggauta kai dauki wuraren da lamarin ya faru, kuma ta tura tawagogin sintiri domin ceto wadanda suka makale.
“Ko da yake an samu rushewar gine-gine guda takwas, amma ba a samu rasa rai ba.
“Domin hana barkewar tashin hankali ko fashi, rundunar ta girke jami’anta a wuraren da ake kwashe mutane don kare dukiyoyinsu daga barayin da ka iya amfani da wannan damar.”
Hotunan ambaliya a Maiduguri
Duba hotunan barnar da albaliyar ta yi a kasa:
News Central TV ma ta wallafa wasu hotuna na irin barnar da ambaliyar ta yi a shafinta na X.
Mutane sun fara barin gidajensu a Borno
Tun da fari, mun ruwaito cewa ruwan sama mai karfi ya haddasa ambaliya a Maiduguri babban birnin jihar Borno, wanda ya tilasta mazauna da dama barin gidajensu.
Yankunan da abin ya fi shafa sun hada da Damboa Road, Moduganari Ngomari da Bulumkutu Abuja.
Wannan lamari na baya-bayan nan ya faru ne shekara guda bayan wata ambaliya makamanciyar wannan ta raba fiye da mutum miliyan daya da gidajensu a Maiduguri.
Asali: Legit.ng

