Borno: Mamakon Ruwa Ya Gigita Jama'a, Mutane Sun Fara Barin Gidajensu
- Wasu mazauna birnin Maiduguri sun tsere daga gidajensu a ranar Laraba sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da ya haifar da ambaliya
- Mazauna unguwanni kamar titin Damboa, Moduganari Ngomari da Bulunkutu Abuja ne suka fi fuskantar matsalar
- Wasu sun nemi mafaka wurin ‘yan uwa da abokai saboda tsoron sake fuskantar bala’i irin na bara
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Maiduguri – Wasu mazauna Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun tsere daga gidajensu a ranar Laraba sakamakon ambaliya.
An samu mummunan ambaliyar bayan da aka samu ruwan sama mai ƙarfi da ya ɗauki sama da awa uku yana zuba.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ambaliyar ta fi shafar unguwanni kamar Damboa Road, Moduganari Ngomari, Bulunkutu Abuja da wasu sassa na Maiduguri.

Kara karanta wannan
Hotuna: An ga yadda ambaliyar ruwa ta rusa gidaje a Borno, mutane sun fara hijira
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu mummunar ambaliya a Borno
BBC Hausa ta wallafa cewa wasu daga cikin mazauna sassan Borno sun yi gaggawar barin gidajensu don neman mafaka wurin 'yan uwa da abokai.
Wani mazauni na Damboa Road, a bayan gidan Indimi, ya shaida cwa suna cikin fargabar yiwuwar sake fuskantar ambaliya mai muni kamar yadda ya faru a bara.
A cewarsa:
"A da, abin da muke fuskanta shi ne ruwa ya taru a wani wuri bayan ruwa ya sauka. Amma na yau ya ba mu mamaki domin ba daga tafki ya zo ba."
"Ka duba can, ruwa ya shiga gidan nan. Ina da tabbacin mazauna gidan sun tsere. Gidanmu ma ruwa na daf da shiga. Haka lamarin ya fara bara kafin ya ƙara tsananta a baya."
Gwamnatin Borno ta tabbatar da aukuwar ambaliya
Wani jami’i daga gwamnatin jihar ya tabbatar da cewa cibiyar kula da lafiya a matakin farko da ke Ngomari na fuskantar barazana saboda ambaliya.

Source: Getty Images
A cewarsa:
"An shirya ƙaddamar da shirin UNICEF da hukumar kula da lafiya ta jihar Borno na rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai a Ngomari PHC da ke bayan asibitin Umoru Shehu a karamar hukumar Jere, amma an dage kaddamarwar saboda ambaliyar da ta mamaye wurin."
Wannan lamari na zuwa ne watanni 10 bayan wata ambaliya mai tsanani ta kashe fiye da mutane 300 tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu a birnin Maiduguri da kewaye.
Yayin da damina ke kara tsananta, mazauna da direbobi na kira ga hukumomi da su dauki matakin gaggawa domin daƙile matsalar da rage illar ambaliya a yankin.
Dalilin ambaliya a jihar Borno
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da cewa ambaliyar da ta mamaye dubunnan gidaje a birnin Maiduguri yayin da jama'a ke neman tsira.
Gwamnatin ta ce lamarin ya samo asali ne daga cika da fashewar madatsar ruwa ta Alau, sakamakon mamakon ruwan sama da aka shafe mako ana yi a yankin.
Wannan na zuwa ne yayin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aika saƙon ta'aziyya da goyon baya ga Gwamna Babagana Umara Zulum da jama'ar jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
