"Lokaci Ya Yi" Gwamnatin Tinubu Ta Yiwa Ƴan Bindiga 'Tayi' a Arewacin Najeriya
- Gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana cewa lokaci ya yi da ƴan bindigar da suka addabi ƴan Arewa za su tuba su daina yin ta'addanci
- Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ya gargarɗi ƴan ta'adda su miƙa makamansu domin samun zaman lafiya a Arewa
- Ribaɗu ya ce gwamnatin tarayya ta yi matukar kokarin a ɓangaren yaki da matsalar tsaro tun daga lokacin da ta karɓi mulki a 2023
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta ba ƴan bindiga damar miƙa wuya domin tabbatar da zaman lafiya a Arewa.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gargaɗi ‘yan bindiga da ke addabar jama'a a Arewacin Najeriya da su mika wuya kuma su daina kashe fararen hula.

Kara karanta wannan
'Ban da Peter Obi': An yi wa Malami wahayi game da mutum 3 da za su fatata a 2027

Asali: Facebook
Gwamnatin Tinubu ta ba ƴan bindiga dama
Malam Nuhu Ribadu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya bayyana wasu nasarori da gwamnatin Tinubu ta samu a fannin tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Mun yi imani cewa lokaci ya yi da waɗannan ‘yan ta’adda za su daina wannan aika-aika su kuma ajiye makamansu, su daina abin da suke yi,” in ji Ribadu.
Duk da wannan gargaɗi, Ribadu ya ce gwamnatin Tinubu ta samu nasarori da dama a ƙoƙarin dakile barazanar tsaro, musamman wajen rage hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban na ƙasar.
Sai dai ana ganin kalaman Nuhu Ribaɗu na zuwa ne a daidai lokacin da sha'anin tsaro ke ƙara lalacewa a wasu sassan Najeriya musamman yankin Arewa.
Har yanzu ana ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, da kuma barazanar da Boko Haram ke haifarwa.

Kara karanta wannan
"Ƴan Arewa ba su yi nadama ba," Minista ya faɗi abin da ke faruwa a gwamnatin Tinubu
Wasu nasarori gwamnatin Tinubu ta samu?
A hirar da aka yi da shi, wacce Daily Trust ta tattaro, Ribadu ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta fara bayyana wa duniya irin ci gaban da ta samu a fannin tsaro.
“A da can, ‘yan ta’adda sukan kai hari kan gidajen gyaran hali, jiragen ƙasa da sansanonin sojoji, amma tun da wannan gwamnati ta karɓi mulki, mun yi nasarar kawo ƙarshen hakan."
“Babu wani babban hari na ta’addanci da aka samu a irin waɗannan muhimman wurare tun bayan da muka hau mulki, ban da a wasu sassan jihar Borno,” inji shi.

Asali: Facebook
An kashe hatsabiban ƴan bindiga 300
Malam Ribadu ya kara da cewa jami'an tsaron Najeriya sun yi nasarar kashe wasu daga cikin manyan hatsabiban ‘yan bindiga.
“Mafi ƙarancin adadin manyan shugabannin ‘yan bindiga da muka kashe ya kai 300. Yanzu mutane da dama sun koma gonakinsu, kuma wuraren da a baya ba a zuwa saboda matsalar tsaro, yanzu an buɗe su," in ji shi.
Nuhu Ribaɗu ya ce hare-hare sun ragu
A wani labarin, kun ji cewa Malam Nuhu Ribaɗu ya bayyana yadda gwamnatin Bola Tinubu ta rage matsalar tsaron da ta damu Najeriya cikin shekaru biyu.
Ribadu ya bayyana cewa hare-haren Boko Haram, ta'addancin 'yan bindiga da rikice-rikicen kabilanci a Arewacin Najeriya sun ragu sosai.
A cewarsa, matsalar tsaro ta ragu matuƙa idan aka kwatanta da yadda abubuwa suka taɓarɓare a gwamnatin da ta gabata.
Asali: Legit.ng