Ana Korafi, Tinubu Ya ba 'Dan Arewa Shugaban Hukumar Kashe Gobarar Najeriya

Ana Korafi, Tinubu Ya ba 'Dan Arewa Shugaban Hukumar Kashe Gobarar Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da nada Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon shugaban hukumar kashe gobara ta kasa
  • Hukumar CDCFIB ta bayyana cewa mai jagorantar hukumar, Abdulganiyu Olola zai yi ritaya nan da kwanaki bayan cika shekaru 60
  • Gwamnatin jihar Kogi ta jinjinawa Bola Tinubu kan nadin Olumode, tana mai cewa ya nuna bajinta da hazaka a fannin gudanar da aiki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon shugaban hukumar kashe gobara ta kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa sabon shugaban hukumar zai fara aiki daga ranar 14 ga watan Agusta, 2025.

Sabo shugaban hukumar kashe gobara, Olumode Adeyemi
Sabo shugaban hukumar kashe gobara, Olumode Adeyemi. Hoto: Kogi State Government
Source: Facebook

Tribune ta wallafa cewa sanarwar nadin ta fito daga sakataren hukumar kula da tsaron cikin gida (CDCFIB), Manjo Janar AM Jibril (mai ritaya), a ranar Laraba, 29 ga watan Yuli, 2025.

Kara karanta wannan

Siyasa: Rikici ya yi kamari a SDP, an tura mutanen El Rufa'i kurkuku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon shugaban zai karbi ragama daga Engr. Abdulganiyu Jaji Olola, wanda zai yi ritaya ranar 14 ga watan Agusta bayan kammala shekarun aiki da suka kai 60.

Tarihin aikin Olumode Adeyemi

Olumode Adeyemi ya fara aikin kashe gobara ne a hukumar FCT kafin ya koma hukumar ta kasa, inda ya zama matakin mataimakin shugaban hukumar (DCG) a sashen kula da ma'aikata.

A yayin aikinsa, ya halarci dukkan kwasa-kwasai na tilas da ake bukata a wajen aiki da kuma wasu taruka da horo a cikin gida da waje.

Haka kuma, Olumode Adeyemi mamba ne a kungiyoyin kwararru da dama ciki har da a ANAN da sauransu

Sakon godiya ga shugaban da zai sauka

Hukumar CDCFIB ta bayyana godiyarta ga shugaban da ke shirin yin ritaya, Abdulganiyu Jaji Olola, bisa kokarinsa wajen cigaban hukumar.

Ta bayyana cewa ya gabatar da shirye-shirye da dama masu amfani, musamman a zamanin shugabancinsa.

Hakanan, hukumar ta bayyana cewa ya nuna kishin kasa da jajircewa wajen aiki, inda ya bar tarihi mai kyau.

Kara karanta wannan

2027: Ana lallaba Atiku da sauran 'yan Arewa su hakura sai Tinubu ya yi tazarce

Jihar Kogi ta yaba wa Bola Tinubu

Gwamnatin jihar Kogi ta fitar da jawabin taya murna ga Olumode Adeyemi Olumode, inda ta bayyana cewa nadin nasa ya nuna yadda mutanen jihar ke da hazaka da cancanta.

Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana cewa wannan nadin ya kara daga darajar jihar Kogi a idon duniya.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta goyi bayan sabon shugaban a sabuwar rawar da zai taka a matakin kasa.

Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo. Hoto: Kogi State Government
Source: Facebook

Gwamnatin jihar ta gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa yadda ya ci gaba da nuna amincewa da mutanen jihar Kogi wajen bayar da gudumawa a cigaban kasa.

Jawabin ya nuna cewa wannan nadin wata alama ce ta irin kwazon da Olumode ke da shi da kuma yadda Kogi ke da mutanen da za su iya rike manyan mukamai na kasa.

Akume ya ce Tinubu bai ware Arewa ba

A wani rahoton, kun ji cewa sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya ce shugaba Bola Tinubu yana damawa da Arewa.

Kara karanta wannan

An gano miliyoyin da aka tara domin tallata Tinubu a zaben 2027

Akume ya bayyana cewa Bola Tinubu ya ba da dama daga cikin 'yan Arewa manyan mukamai a gwamnatinsa.

Baya ga haka, ya ce shugaban yana gudanar da muhimman ayyuka da suka shafi Arewa kai tsaye tun bayan fara mulki a 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng