Sanatocin Arewa Sun Yi Tir da Kisan Mutane a Zamfara, an Aika Sako ga Tinubu
- Kungiyar sanatocin Arewa ta fito ta yi tir da kisan kiyashin da aka yi wa wasu mutane a jihar Zamfara kwanan nan
- Shugaban kungiyar, Abdul'aziz Musa Yar'adua ya yi Allah wadai da kisan, ya bayyana cewa hakan ba dabi'ar mutanen Arewa ba ce
- Sanatan ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kara kan kokarin da yake yi wajen tabbatar da tsaro a yankin Arewa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Kungiyar Sanatocin Arewa ta yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon baya da yake ci gaba da bai wa hukumomin tsaro.
Kungiyar 'yan majalisar ta bayyana cewa har yanzu akwai bukatar a kara zage damtse domin shawo kan karuwar rashin tsaro a yankin Arewa.

Source: Twitter
Shugaban kungiyar, Sanata Abdulaziz Yar’adua, ne ya bayyana hakan a martaninsa kan kisan da aka yi wa akalla mutane 35 a karamar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin, inda suka kashe wasu daga cikinsu duk da cewa an biya kudin fansa.
Me sanatocin Arewa suka ce kan kisan Zamfara?
Abdul'aziz Yar’adua ya bayyana kisan da cewa “mummunan aiki ne” wanda bai dace da dabi’u ko halayen yankin Arewa ba.
"Muna Allah-wadai da wannan mummunan aiki da kakkausar murya, kuma muna bayyana cewa hakan ba shi ne abin da ke wakiltar dabi’u, mutane da buri na yankin Arewa ba."
"Yankinmu ya shahara da karimci, zaman lafiya da natsuwa, kuma irin waɗannan ayyukan tashin hankali na lalata abubuwan da muke alfahari da su."
- Abdul'aziz Musa Yar'adua
Yar'Adua mai wakiltar Katsina ta tsakiya bukaci hukumomin tsaro da su karfafa hadin gwiwa da kungiyoyin sa-kai na cikin gida da kuma inganta tattara bayanan sirri domin hana sake faruwar hare-haren.
Sanata Abdul'aziz Yar’adua ya nuna alhini tare da jajantawa ga al’ummar jihar Zamfara da kuma iyalan wadanda abin ya rutsa da su, rahoton The Punch ya tabbatar.
"Muna rokon Allah ya gafarta wa wadanda suka rasa rayukansu tare da ba iyalansu hakurin jure wannan babban ibtila’i.”
- Abdul'aziz Musa Yar'adua

Source: Original
An aika sako ga Shugaba Tinubu
Ya yaba da ci gaba da goyon bayan da Shugaba Tinubu ke bayarwa a bangaren tsaro, ciki har da samar da kudu da daukar sababbin jami’ai da dama.
Sai dai ya jaddada cewa akwai matukar bukatar a kara horar da jami’an tsaro tare da inganta hadin kai da tsari a aikace.
"Muna fatan cewa za a kara yawan horas da jami’an tsaro domin hana faruwar irin wannan lamari nan gaba."
- Abdul'aziz Musa Yar’adua
An bukaci gwamnan Zamfara ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar ZGGF ta taso Gwamna Dauda Lawal na Zamfara a gaba kan sai ya yi murabus daga kujerarsa.
Kungiyar ta zargi gwamnan da rashin kwarewa wajen gudanar da shugabancin jihar Zamfara sakamakon hare-haren 'yan bindiga.
Ta bayyana cewa idan aka samu sauyin shugabanci, za a iya samun sabon jini da tsari mai kyau a kokarin kawo karshen 'yan bindiga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

