Ruwa da Iska Mai Ƙarfi Sun Kifar da Jirgi bayan Ya Ɗauko Fasinjoji a Jihar Jigawa

Ruwa da Iska Mai Ƙarfi Sun Kifar da Jirgi bayan Ya Ɗauko Fasinjoji a Jihar Jigawa

  • Wani jirgin ruwa ya gamu da hatsari a kauyen Zangwan Maje da ke ƙaramar hukumar Taura a jihar Jigawa
  • Kwale-kwalen wanda ya ɗauko ƙananan yara 15 ya kife ne bayan ya taso daga Jejin Gunka zuwa Zangwan Maje ranar Lahadi
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum shida, tare da ceto bakwai a raye, har yanzu ana ci gaba da laluben ragowar mutum biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mutane shida, yayin da har yanzu ake neman wasu biyu a kauyen Zangwan Maje, karamar hukumar Taura, jihar Jigawa.

Rundunar ƴan sanda reshen jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar hatsarin jirgin ruwan na gargajiya a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, 29 ga watan Yuli, 2025.

Jirgin ruwa ya gamu da hatsari a Jigawa.
An rasa rayuka da wani kwale-kwale ya kife a jihar Jigawa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 27 ga Yuli, 2025, lokacin da kwale-kwale da ke dauke da yara 15 daga gonar Jejin Gunka zuwa ƙauyensu ya kife a ruwa, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'adda Sun Kwace Ikon Karamar Hukuma a Plateau? Gwamna Mutfwang Ya Yi Bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ruwa da iska sun haddasa hatsarin jirgi

Bayanai sun nuna cewa kwale-kwale ya kife a ruwan ne sakamakon ambaliya, iska mai karfi da kuma yadda aka cika shi maƙil fiye da kima.

‘Yan sanda sun ce an ceto yara bakwai da ransu, yayin da aka gano gawawwaki guda shida zuwa safiyar Talata, sannan ana ci gaba da neman sauran yara biyu da suka bace.

Sanarwar ta ce yaran da aka ceto su ne, Rukayya Abdullahi (9), Ibrahim Garba (12), Fatima Yusuf (10), Suwaiba Yahaya (20), Rukayya Saleh (18), Jawahira Samaila (10) da Sakina Sule (11).

Waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu sun hada da, Hare Abdullahi (12), Halima Ma’azu (12), Nasiba Yahya (15), Saima Yusuf (25), Amina Sule (11), da Saiya Abdullahi (18).

Ƴan sanda na neman direban kwale-kwale

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar, SP Shi’isu Lawan Adam, wanda ya sa hannu a cikin sanarwar, ya bayyana cewa direban kwale-kwalen ya tsere daga wajen hadarin.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama bindigogi ana kokarin kai su Kano daga Filato

“Ana kokarin gano inda yake domin kama shi da gurfanar da shi a gaban kotu a matsayin izina ga wasu,” inji shi.
Jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya.
Yan sanda sun barazana neman matuƙin jirgin da ya yi hatsari a Jigawa Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Ƴan sanda sun ja hankalin mazauna Jigawa

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Dahiru Muhammad, ya bayyana alhini kan wannan lamari, tare da mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu da kuma daukacin al’ummar Zangwan Maje.

“Mun shiga jimami matuka kan wannan ibtila’i. Ina rokon mazauna yankunan da ke kusa da koguna da su guji tafiye-tafiye da dare.
"Kuma mutane su daina cika ƙananun kwale-kwale fiye da kima, sannan su tabbata suna amfani da rigar kariya a koda yaushe,” inji CP Muhammad.

Mutanen da suka iya ruwa, ‘yan sanda da ma’aikatan agaji suna ci gaba da bincike don nemo sauran yara biyu da suka ɓace, rahoton Daily Trust.

Jirgin ruwa ya yi hatsari a jihar Neja

A wani labarin, kun ji cewa wani jirgin ruwa ya yi hatsari a yankin ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja ranar Asabar.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce mutane da dama sun rasa rayukansu.

Jirgin ruwan, wanda ke ɗauke da adadin da ba a tantance ba na fasinjoji da kaya, ya kife ne a hanyarsa ta zuwa kasuwar Kwata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262