'Yan Ta'adda Sun Kwace Ikon Karamar Hukuma a Plateau? Gwamna Mutfwang Ya Yi Bayani

'Yan Ta'adda Sun Kwace Ikon Karamar Hukuma a Plateau? Gwamna Mutfwang Ya Yi Bayani

  • Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya tabo batun maganar 'yan ta'adda sun karbe iko da wani yanki na jihar suna cin karensu babu babbaka
  • Caleb Mutfwang ya bayyana cewa a duk fadin jihar, babu wata karamar hukuma da karkashin ikon 'yan ta'adda ko 'yan bindiga
  • Gwamnan ya nuna cewa tun bayan hawansa kan madafun iko, ya dauki kwararan matakai don ganin an samu ingantaccen tsaro a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa babu wata ƙaramar hukuma a jihar da ‘yan bindiga ko ‘yan ta’adda ke iko da ita.

Gwamna Mutfwang ya yi wannan bayani ne yayin wani taron tattaunawa da ‘yan jarida da aka gudanar a sabon gidan gwamnati da ke Jos a jiya Talata.

Gwamnan Plateau ya yi magana kan rashin tsaro
Gwamnan Plateau ya ce jihar ta fi wasu jihohin Arewa tsaro Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ya bayyana matakan da gwamnatinsa ta ɗauka domin magance matsalolin tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Shugaban gwamnoni 19 ya fadi ya fadi abin da 'yan Arewa za su yi kan tazarcen Tinubu

Wane hali tsaro ke ciki a Plateau?

Gwamna Mutfwang ya jaddada cewa duk da hare-haren da ake samu a wasu yankuna kamar Riyom, Bokkos, Bassa, Kanam, da Mangu, gwamnati ta samu ci gaba fiye da yadda wasu rahotanni na kafofin watsa labarai ke bayyanawa.

Ya ce sabanin yadda duniya ke kallon lamarin, Jihar Plateau tana da tsaro fiye da wasu jihohi a Arewa kamar su Zamfara, Neja, Sokoto, Nasarawa, Katsina da Kebbi.

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa tun da aka rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023, ya kafa kwamitin tsaro domin bincika matsalolin tsaro da suka dade suna addabar jihar tare da samar da hanyoyin magance su.

Ya ce kwamitin da ya kafa na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa tsaro ya inganta matuƙa a jihar, rahoton Daily Post ya tabbatar da wannan.

Haka kuma, ya yi alƙawarin farfaɗo da rundunar Operation Rainbow domin ta taimaka wa Operation Safe Haven, rundunar sojoji da aka kafa domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta dukufa a kan ilimi, ta gyara fiye da makarantu 1,200 a sassan jihar

Gwamna Mutfwang na kula da ma'aikata

Gwamnan ya kuma bayyana cewa ya bai wa walwalar ma’aikata muhimmanci a jiharsa.

"Ma’aikatanmu sun dawo da mutuncinsu. Mun dawo da ƙima da karsashi a cikin ma’aikatan jihar Plateau."

- Gwamna Caleb Mutfwang

Gwamna Mutfwang ya ce an samu tsaro a Plateau
Gwamna Mutfwang ya ce yana kokari kan tsaro a Plateau Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

Karanta karin wasu labaran kan jihar Plateau

'Yan bindiga sun hallaka manoma a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci kan manoma a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun hallaka manoma 27 a harin da suka kai a yankin Bindi-Jebbu na kauyen Tahoss a karamar hukumar Riyom.

Wasu mazauna yankin sun dora alhakin kai harin kan 'yan bindiga na Fulani inda suka ce sun rika harbi kan mai uwa da wabi tare da kona gidaje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng