Fadar Shugaban Kasa Ta Kalubalanci Masu Sukar $100,000 da Gidajen da Tinubu Ya ba Falcons
- Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya ce ba laifi ba ne a bai wa ‘yan wasan Super Falcons $100,000 ba
- Kowace ƴar wasan Super Falcons ta ya samu kyautar Daloli da suka kai N150m, da kuma lambar girmamawa ta OON
- Lamarin ya jawo maganganu a tsakanin ƴan Najeriya da ke ganin kyautar ta yi yawa idan aka duba halin da wasu ma'aikata ke ciki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya kare kyaututtuka da kuɗin da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ‘yan wasan Najeriya na Super Falcons.
Kowace ƴar wasa ta samu lambar yabo ta kuɗi aƙalla N150m yayin da kowanne ɗan kwamitin horaswa na ƙungiyar ya samu aƙalla N75m da gidaje a Abuja

Source: Facebook
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, Onanuga ya mayar da martani ga masu sukar kyaututtukan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu daga cikin ƴan Najeriya dai na ganin cewa kyautar ta yi yawa, ganin cewa suna karɓar albashi da kuma halin da ƙasa ke ciki.
Onanugu ya kare kyautar Tinubu ga Falcons
A cikin saƙon, Onanuga ya kwatanta kyautar da Tinubu ya bayar da wacce ake samu a BBNaija idan an kammala shirin.
Ya ce:
“Idan ka tuna cewa Multichoice, masu shirya wasan BBNaija, na bai wa wanda ya yi nasara Naira miliyan 150 a matsayin kyauta, na yi mamakin dalilin da yasa wasu ‘yan Najeriya ke nuna rashin gamsuwa da kyautar da Shugaba Tinubu ya bai wa Super Falcons.”
“Shugaba Tinubu ya karrama ƙwazo, jajircewa, ƙwarewar ƙwallon ƙafa da fito da Najeriya Najeriya."

Source: Twitter
Bayan tarbar tawagar Super Falcons a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Tinubu ya kuma ba su lambar girmamawa ta OON bayan nasararsu a gasar ƙwallon ƙafa ta Afrika.

Kara karanta wannan
Ba kunya ba tsoron Allah, matashi ya yaudari surukarsa ya caka mata adda har lahira
Falcons: Jama'a sun dura kan hadimin Tinubu
Kwatanta kyautar da aka bai wa Super Falcons da ta BBNaija da Onanuga ya yi ya haifar da muhawara a dandalin X, inda jama’a da dama suka bayyana ra’ayoyinsu game da hakan.
Wani mai amfani da X, @Wale_Abdul, ya ce:
“Me ya sa ake basu kuɗin a Dala? Mafi arzikin ƙasashe a duniya ba za su bayar da Dala ga ‘yan wasa da ke karɓar albashi ba.”
@Bolanle_Juwon ya bayyana cewa:
“Me ya sa ba a bai wa ‘yan wasan a kyautar a Naira ba? Ya kamata gwamnatin Najeriya ta daina tallata kuɗin wata ƙasa.”
Shi kuma @Daroking ya ce:
“Wannan ‘Sanata Bola Ahmed Tinubu’ da ake ce wa shugaban ƙasa fa? Ko da yake ina murna da nasararsu, duk siyasa ce. Muna da sojoji da ‘yan sanda da ake biyansu ƙasa da mima, su ma sun cancanci kulawa.”
Tinubu ya gwangwaje Super Falcons
A baya, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya karrama ‘yan wasan Super Falcons bayan sun lashe gasar cin kofin mata na Afrika (WAFCON) karo na goma 10.
A cikin girmamawar da ya basu, kowacce ‘yar wasa daga cikin 24 ta samu kyautar dala $100,000 (kimanin N152.8 miliyan), tare da gida mai ɗakuna uku.
Shugaban ya bayyana hakan ne a taron karɓar ‘yan wasan da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, kamar yadda hadiminsa Olusegun Dada ya tabbatar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

