Ana Rigimar Sauya Sunan UNIMAID, Jami'ar Ta Karrama Tinubu yadda Ya Yi ga Buhari
- Asibitin koyarwa na jam'iar Maiduguri ya bude cibiyar fasahar zamani na ICT ta kiwon lafiya kuma sai aka karrama Bola Tinubu
- An sanyawa cibiyar da aka bude ta musamman sunan shugaban kasa wacce ta koma 'Bola Ahmed Tinubu Medical ICT Institute'
- Hakan na zuwa ne yayin da ake tsaka da rigimar sauya sunan jami'ar zuwa sunan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Ba a gama da tuhumar sauya sunan UNIMAID ba, an karrama Bola Tinubu a jami'ar Maiduguri.
Hukumar asibitin koyarwa na jami’ar da ke jihar Borno, ta karrama Tinubu inda ta sanya sunan sabon ginin cibiyar ICT saboda shi.

Source: Facebook
UNIMAID: Jami'ar Maiduguri ta karrama Tinubu
Rahoton Punch ya ce an sanya sunan cibiyar ta lafiya da aka kammala da sunan 'Ahmed Tinubu Medical ICT Institute'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bikin kaddamarwar ya kasance wani bangare na wani babban taro karo na 110 na Likitoci wanda ya gudana a Maiduguri ranar Talata.
A jawabinsa kafin bude cibiyar, Daraktan Asibitin, Ahmed Ahidjo, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa tallafin da ta bayar wajen kafa wannan gagarumar cibiyar.
Ya ce:
“Ministan lafiya, Ali Muhammad Pate, ya nuna cewa abubuwa da dama na iya yiwuwa, Muna samun dukkan abin da muke nema daga Gwamnatin Tarayya.
“Yau muna bude cibiyar ICT ta lafiya ta farko a Najeriya, wadda aka saka wa suna Bola Tinubu domin nuna godiya."

Source: Twitter
Za a karrama mutanen da ke taimakon al'umma
Ya kara da cewa akwai wasu ayyuka guda takwas da suka hada da tituna, asibitoci da gine-gine da aka ware wa wasu manyan masu taimakon al'umma.
Ministan lafiya, Ali Pate ya bayyana cewa fannin lafiya na daya daga cikin muhimman ginshikai na gwamnatin Shugaba Tinubu da ke kawo sauyi a fadin kasa.
Ya ce:
“A cikin shekaru biyu na mulkin Tinubu, ya mayar da fannin lafiya matsayin jigo a tsare-tsarensa kuma sakamakon yana bayyana.
“A yau, a kowane asibitin gwamnatin tarayya zaka samu akalla aiki daya ko biyu da aka kammala ko kuma ana ci gaba da aiwatarwa.”
Ya yabawa kungiyar daraktocin likitoci bisa jagorancin da suke bayarwa, yana mai cewa suna taka rawa matuka wajen tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya.
“Ina matukar jin dadin kasancewa a cikin ku yau, yana da kyau asibitin ya hada wannan bikin da kaddamar da muhimman ayyuka da dama.
“Ina gode wa gwamnatin jihar Borno da al’ummar jihar saboda kyakkyawar tarba da kuma rawar da suka taka wajen tallafawa wannan gini."
- Ali Pate
Taron ya samu halartar gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, mataimakinsa Usman Kadafur, sarakunan gargajiya da 'yan majalisa daga matakin jiha da tarayya.
Dalibi a UNIMAID ya tattauna da Legit Hausa
Mukhrar Goni da ke tsangayar ilimin kiwon lafiya ya ce wannan ba shi ne damuwarsu ba.
Ya ce:
"Don UMTH ta sauya sunan wata cibiya zuwa na Tinubu ba matsala ba ne.
"Babban damuwa a wuri na shi ne sauya sunan UNIMAID kacokan zuwa Muhammadu Buhari University."
Ya ce abin bai yi wa dalibai da wasu malamai da dama dadi ba ko kadan.
ASUU ta kalubalanci sauya sunan UNIMAID
Mun ba ku labarin cewa kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU reshen jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno ta shirya shiga kafar wando daya da shugaban kasa, Bola Tinubu.
Kungiyar ta ce za ta kai gwamnatin kotu saboda sauya sunan jami’ar zuwa 'Muhammadu Buhari University' ba tare da tuntubar ta ba.
Malaman sun bayyana sauya sunan a matsayin rashin girmama ikon jami’a, rashin tuntuba da cin zarafin tarihin shekaru 50 na jami’ar.
Asali: Legit.ng


