Shugaban Gwamnoni 19 Ya Fadi Abin da 'Yan Arewa za Yu Yi kan Tazarcen Tinubu

Shugaban Gwamnoni 19 Ya Fadi Abin da 'Yan Arewa za Yu Yi kan Tazarcen Tinubu

  • Gwamna Inuwa Yahaya ya ce Bola Tinubu ya fara cika alkawurran da ya dauka a 2023 musamman kan manyan ayyuka da tsaro
  • Inuwa Yahaya ya jero muhimman ayyukan da ke gudana a Arewa kamar titin Abuja-Kaduna-Kano da aikin mai a Kolmani
  • Ya ce hadin gwiwa tsakanin gwamnati da jama'ar kasa zai tabbatar da dorewar dimokuradiyya da cigaban Arewa baki daya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Gombe kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya, ya tabbatar da cewa Arewa za ta cigaba da goyon bayan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin bude wani zama na kwanaki biyu da gidauniyar Ahmadu Bello Memorial Foundation ta shirya a Kaduna domin duba yadda gwamnati ke tafiyar da mulki.

Kara karanta wannan

2027: Kungiyar ATT ta samo mafita ga Arewa kan tazarcen Shugaba Tinubu

Wasu daga cikin gwamnonin Arewa a wani taro.
Wasu daga cikin gwamnonin Arewa a wani taro. Hoto: Isma'ila Uba Misilli
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa ya ce taron ya zama wata dama ta tantance ayyukan gwamnati da kuma yadda ake cika alkawurran da aka dauka kafin zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Inuwa ya ce Tinubu na cika alkawura

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya dauki manyan alkawura a lokacin yakin neman zabe a 2023.

A cewar shi:

"A lokacin yakin neman zabe, dan takara Bola Tinubu ya yi alkawurra na musamman ga Arewa.
"Mutanenmu sun yarda kuma sun ba da fiye da kashi 60 na kuri'un da suka kai shi kan mulki."

Ya ce an fara gani a kasa, inda ya lissafa manyan ayyuka kamar titin Abuja-Kaduna-Kano, layin dogo daga Kano zuwa Katsina da Maradi, da farfado da matatar man Kaduna.

Ya kara da cewa ana ci gaba da hakar mai a Kolmani, sannan kuma ana aikin bututun iskar gas daga Abuja zuwa Kano.

Wasu ayyuka da tsare-tsare a Arewa

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya fara gwangwaje jihohin Arewa da titunan jiragen kasa

Gwamnan ya ce ana shirin fara babbar hanyar Sokoto-Badagry da gyaran hanyoyin jihohi, da bunkasa aikin gona da kiwon lafiya, wanda duk suna da nufin farfado da tattalin arzikin Arewa.

Dangane da tsaro kuwa, ya ce fiye da kwamandojin 'yan ta'adda 300 aka hallaka a 'yan watannin nan ta hanyar hadin gwiwar sojoji da jami’an leken asiri, yana mai cewa:

“Ko da yake har yanzu akwai kalubale, an fara karya karfin wadanda ke addabar jama'a.”
Wajen da ake gabatar da taron nazarin nasarorin Tinubu a Kaduna
Wajen da ake gabatar da taron nazarin nasarorin Tinubu a Kaduna. Hoto: Dada Olusegun
Source: Facebook

Bayani kan matsin tattalin da aka shiga

Gwamna Inuwa ya yaba da kirkirar ma'aikatar bunkasa kiwo a matsayin hanya ta zamanantar da tattalin arzikin makiyaya da warware rigingimun makiyaya da manoma.

Game da matakin cire tallafin man fetur da sauya tsarin musayar kudi, ya ce duk da hakan na da radadi ga jama'a, amma matakai ne da za su haifar da daidaiton tattalin arziki a nan gaba.

Ya jaddada bukatar hadin gwiwar gwamnatocin jihohi da sarakuna da shugabannin addini da na kasuwanci wajen ciyar da Arewa gaba da inganta rayuwar al'umma.

Legit ta tattauna da Muhammad Sa'idu

Wani matashi a jihar Gombe, Muhammad Sa'idu ya bayyana wa Legit cewa gwamnan ya yi magana bisa ra'ayinsa ba matsayar 'yan Arewa ba.

Kara karanta wannan

'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'

Muhammad ya ce:

"Wata kila ita ce matsayar da gwamnonin Arewa suka dauka tunda shi ne shugabansu. Amma mu kam ba mu yi haka da wani shugaba ba.
"Har yanzu ba ni da matsaya a kan wanda zan zaba, sai lokaci ya yi tukuna."

An ba Atiku matsayin jagoran Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo da ke wakiltar Gombe ta Arewa a majalisar dattawa ya yaba wa Atiku Abubakar.

Sanata Dankwambo ya ce Atiku Abubakar ne shugabansu a harkokin siyasa duk da cewa ya fita daga jam'iyyar PDP.

Ya yi bayanin ne yayin wani taron jam'iyyar PDP da aka yi a jihar Gombe bayan daura auren 'yar shi a ranar Asabar da ta wuce.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng