Gwamnatin Kano Ta Dukufa a kan Ilimi, Ta Gyara Fiye da Makarantu 1,200 a Sassan Jihar
- Gwamnatin Kano ta bayyana cewa tana kan bakarta na tabbatar da dawo da martabar ilimi a dukkanin sassan jihar
- Ta ce zuwa yanzu, ta gyara fiye da makarantu 1,200 a ƙananan hukumomi 44, bayan haka kuma ta yi gyara a sassan Kano
- Haka kuma ta ware N3bn don gyaran makarantu 13 na ’yan mata da aka rufe a baya, a wani yunkuri na dawo da darajar ilimi a jihar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta kammala gyaran makarantu sama da 1,200 a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Kwamishinan ilimi na jihar, Dr. Ali Haruna Makoda, ne ya bayyana hakan yayin taron bita na kwana guda kan ingancin ilimi, a jihar Kano.

Source: Facebook
Radio Nigeria Kaduna ta ruwaito cewa Dr. Ali Makoda ya bayyana cewa wannan aikin gyara yana daga cikin muhimman matakai da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke ɗauka domin farfaɗo da ilimi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Abba tana gyaran makarantu a Kano
Jaridar Daily Nigerian ta ƙara da cewa an ware Naira miliyan 484 domin aikin gyaran makarantu a mazabu 484 a fadin jihar.
A cewarsa:
“Tun daga hawan wannan gwamnati, an gyara fiye da makarantu 1,200 a faɗin ƙananan hukumomi 44."
"Haka kuma, ana ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a mazabu daban-daban karkashin wakilan kansiloli da kuɗinsu ya kai N484m.”
Dr. Makoda ya bayyana cewa wannan shiri na gyara makarantu yana daga cikin ayyana dokar ta-baci da gwamnatin jihar ta ayyana a fannin ilimi a watan Mayun 2024.
Gwamnan Kano ya fadi manufarsa kan ilimi
Kwamishinan ya ƙara da cewa ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi na nuni da ƙudurin Gwamna Abba Kabir Yusuf na dawo da darajar ilimi a jihar, bayan tabarbarewar da aka samu a baya.

Kara karanta wannan
Kano: An ɗauki mataki a kan dabbobin dawan gidan tsohon Akanta bayan mesa ta tsere
Ya kuma tuna cewa gwamnatin jihar ta amince da Naira biliyan 3 domin gyara makarantu 13 na ‘yan matan je ka ka dawo da na kwana, waɗanda gwamnatin da ta gabata ta rufe.

Source: Facebook
Dr. Makoda ya jaddada cewa Jihar Kano na da fiye da makarantu 30,000, mafi yawa a cikin dukkannin jihohin Najeriya.
Ya nanata cewa gwamnati na da ƙudurin ganin kowanne yaro ya samu ingantaccen ilimi cikin daidaito da adalci.
Gwamnan Kano ya ziyarci makarantar sakantare
A baya, mun wallafa cewa gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara ta gaggawa zuwa makarantar Kano Day Science College, da ke a ranar Litinin, 29 ga Yuli, 2025.
Ziyarar ta zo kasa da kwana guda bayan da Ɗan Bello ya fitar da wani bidiyo da ya dauki hankalin jama'a, wanda ke bayyana mummunan halin da makarantar ke ciki ta fuskoki da dama.
A cikin bidiyon, Ɗan Bello ya nuna yadda dalibai ke fama da rashin kujeru, karancin kayan koyo da koyarwa, da kuma mummunan yanayin banɗaki mara tsafta da rashin ruwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
