Gwamna Ya Dakatar da Hadiminsa, Ya Kori Ahmed Musa daga Shugabancin Hukumar EDOFEWMA
- Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya dakatar da hadiminsa, Felix Isere bisa zargin haɗa kuɗaɗe ba tare da neman izini ba
- Okpebholo ya kuma kori Ahmed Musa daga matsayin shugaban hukumar EDOFEWMA tare da maye gurbinsa da Arch. Fashanu Emmanuel
- Wadannan matakai biyu sun fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin jihar Edo, Musa Ikhilor ranar Litinin, 28 ga watan Yuli, 2025
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da Mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin Mai da Iskar Gas, Felix Isere, bisa zargin aikata damfara.
An bayyana dakatarwar ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Musa Ikhilor, ya rattaba wa hannu a ranar Litinin, 28 ga Yuli, 2025.

Source: Twitter
A cewar Ikhilor, an dakatar da hadimin gwamnan ne bayan da ya fara tara kuɗi ba tare da izini ba, domin shirya taron Oil and Gas Summit, kamar yadda Punch ta rahoto.
Musa Ikhilor ya bayyana cewa gwamnatin Okpebholo ba ta amince da shirya wannan taron ba kuma ba ta bada izinin neman gudummawa ba.
Meyasa gwamnan Edo ya dakatar da hadiminsa?
Gwamna Okpebholo ya kuma umarci Felix Isere ya mayar da duk kuɗin da ya karɓa daga hannun masu bada gudummawa.
Sanarwar ta ce:
“Muna sanar da jama’a cewa Gwamnan Jihar Edo, Mai Girma Sanata Monday Okpebholo, ya dakatar da Mai Ba shi Shawara na Musamman kan Harkokin Mai da Iskar Gas, Felix Osemwengie Isere, daga aiki.
"Ya ɗauki wannan matakin ne saboda tara kuɗaɗe ba tare da izini ba, da amfani da sunan Gwamnatin Edo domin shirya taron mai da gas wanda za a yi a Benin, ranar Alhamis 7 ga Agusta, 2025.
“A saboda haka, an soke taron da aka shirya kuma gwamna ya umurci Felix Osemwengie Isere ya mayar da duk wasu kuɗaɗen da ya karɓa daga hannun masu tallafawa.
Gwamna Okpebholo ya dakatar da Ahmed Musa
Har ila yau, Gwamna Okpebholo ya kori Ahmed Musa, daga matsayin Shugaban Hukumar Kula da Ambaliya, Zaizayar Ƙasa da Ruwa ta Jihar Edo (EDOFEWMA).
Gwamnan ya naɗa Arch. Fashanu Emmanuel a matsayin sabon shugaban hukumar EDOFEWMA, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar ta tabbatar.

Source: Facebook
Arch. Fashanu ƙwararren masanin harkokin gini ne, wanda ke da fiye da shekaru 20 na gogewa, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Ya kammala digiri na farko a fannin zanen gini daga Jami’ar Obafemi Awolowo University, Ile-Ife a 1999, sannan ya samu digirin digirgir daga Jami’ar Jos a 2011.
Sanarwar gwamnatin Edo ta ƙara da cewa wannan sabon naɗin ya fara aiki nan take.
Abin lura anan
Wannan mataki da Gwamna Monday Okpebholo ya ɗauka na dakatar da hadiminsa da kuma sauya shugaban hukumar EDOFEWMA na nuna irin jajircewarsa wajen tabbatar da da’a da tsari a cikin gwamnatin sa.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Saurayi ya sari tsohuwar budurwarsa da adda, ya kashe mahaifiyarta
Hakan na nuni da cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci cin hanci, karya doka ko almundahana ba – komai kusancin mutum da shi.
Wasu daga cikin masu sharhi kan al'amuran siyasa sun bayyana cewa irin wannan matsayi na iya zama sako kai tsaye ga sauran jami’an gwamnati da ke da alhakin kula da makudan kudade ko shirya manyan ayyuka, da su kiyaye gaskiya da bin ka'ida.
Al’ummar jihar Edo na sa ran ganin ci gaba a fannin shugabanci, musamman ganin cewa sabon shugaban EDOFEWMA – Arch. Fashanu – na da ƙwarewa da gogewa a bangaren gini da tsare-tsaren muhalli.
Ana sa ran zai kawo sabbin dabaru da ingantattun hanyoyi don rage matsalar ambaliya da zaizayar ƙasa a fadin jihar.
Bayanin da gwamnati ta fitar ya bayyana cewa duk wani taro da ya shafi harkar mai da iskar gas dole ne ya samu izini kai tsaye daga gwamna ko ma’aikatar da ta dace, domin kauce wa rudani da rashin amincewar jama’a.
Gwamna Edo zai tarawa APC ƙuri'u 2.5m
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Edo, Monday Okpebholo ya yi aƙawarin bai wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ƙuri'un miliyan 2.5 a zaɓen 2027.
Monday Okpebholo ya ce zai yi haka ne a matsayin wata hanya ta nuna godiya bisa yadda shugaban ya nuna ƙauna da kulawa ga jihar Edo.
Gwamnan ya sanar da wannan shiri da yake yi ne a wurin taron karɓar sababbin ƴan APC, waɗanda suka sauya sheƙa daga PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


