Zamfara: Gwamna Ya Nada Sabon Sarkin Gusau bayan Rasuwar Mai Martaba
- An nada Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau, domin maye gurbin mahaifinsa, marigayi Dr. Ibrahim Bello
- Sarkin Katsinan Gusau, Mai Martaba Ibrahim Bello, ya koma ga Mahalicci a safiyar ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025 yana da shekara 71
- Gwamnanatin jihar Zamfara ta tabbatar da cewa an yi nadin ne bisa doka da kuma shawarar masu zaben sarki a masarautar Gusau
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da nadin Alhaji AbdulKadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau.
Nadin na nufin domin maye gurbin mahaifinsa, marigayi Dr. Ibrahim Bello, wanda ya rasu kwanan nan bayan shafe shekaru 10 yana mulki.

Source: Facebook
BBC Hausa ta wallafa cewa sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Abubakar Mohammad Nakwada, ya bayyana nadin sabon Sarkin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An nada sabon Sarkin Katsinan Gusau
Channles TV ta wallafa cewa an yi nadin ne bisa shawarar masu zaben sarki na masarautar Gusau, tare da bin dokoki da al’adun gargajiya na jihar.
Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello shi ne ɗa na fari ga marigayi sarki, kuma kafin nadin nasa, yana rike da mukamin gargajiya na Bunun Gusau.
Bunun Gusau na daya daga cikin manyan mukamai a cikin masarautar.
Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna
Gwamna Dauda Lawal ya taya sabon sarki murna tare da kira gare shi da ya ci gaba da gini a kan tarbiyya da mahaifinsa da kakanninsa suka kafa, musamman kasancewarsa jikan Malam Sambo Dan Ashafa.
Gwamnan ya kuma bukaci sabon sarkin da ya zama ginshikin zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a tsakanin al’ummar masarautar Gusau da ma jihar Zamfara gaba daya.
Rasuwar marigayi Sarkin Katsinan Gusau, Mai Martaba Dr. Ibrahim Bello, ta auku ne da safiyar ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025.
Ya rasu yana da shekaru 71 da haihuwa, bayan shekaru 10 yana kan karagar mulki da cike da mutunta jama'a tare da nuna kishin al’ummar da yake wakilta.

Source: Twitter
Gwamna Dauda Lawal da ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar, ya yi addu’ar Allah SWT ya jikan sarkin da rahama kuma ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.
Rasuwar ta gigita jama'a da dama a Arewacin Najeriya, musamman ganin yadda ake rashe-rashen manya a shiyya a cikin 'yan kwanakin nan.
An mutunta wasiyyar Srkin Gusau
A wani labarin, mun wallafa cewa an gudanar da sallar jana’izar Sarkin Katsinan Gusau, Dr. Ibrahim Bello a babban masallacin Juma’a na Gusau, kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Dubbunnan mutane ne suka halarta, ciki har da Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, mataimakinsa Alhaji Mani Mummuni, da manyan ‘yan majalisar dokoki na jiha da na tarayya.
Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan jihar Zamfara, ya tabbatar da cewa an birne marigayin Sarkin Gusau kamar yadda ya bukata ya bukata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

