Dattijon Arewa Ya Hararo Babban Rikici a Najeriya idan aka Yi Magudi a Zaben 2027
- Tsohon mai ba mataimakin shugaban kasa shawara da ya yi murabus ya ce sahihin zabe ne kadai zai hana rikici a 2027
- Hakeem Baba-Ahmed ya ja hankalin INEC da shugabanni su saurari kiraye-kirayen neman gaskiya a zabuka masu zuwa
- Jam’iyyun siyasa da dama sun nuna goyon bayan shirin gudanar da zabe guda daya a rana daya da majalisa ke kokarin kawowa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Dr Hakeem Baba-Ahmed ya gargadi gwamnati da hukumar zabe ta kasa (INEC) da su tabbata sahihancin zaben 2027 domin kaucewa rikici a kasar.
Wasu jam'iyyun siyasa sun bayyana ra'ayoyi kan kokarin da majalisa ta fara na dawo da dukkan zabuka a rana daya.

Source: UGC
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Litinin, inda ya jaddada muhimmancin gudanar da zabe mai gaskiya da adalci a matakin kasa baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gargadin Baba-Ahmed kan magudin zabe
Gargadin Dr Hakeem ya zo ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan sauye-sauyen da majalisar wakilai ke kokarin yi a dokar zabe, ciki har da shirin gudanar da zabuka a rana daya.
A cewar shi:
“An fara magana dangane da amincin zabukan 2027. Ya kamata shugabanninmu da INEC su saurari jama'a.
"Idan aka yi zabe ba tare da gaskiya ba, kowa zai shiga matsala. Magudi zai jefa kasar cikin rikici mafi muni.”
The Guardian ta ce gargadin ya dace da halin da kasar ke ciki da bukatar mayar da hankali wajen dinke barakar da rashin sahihancin zabe ka iya haifarwa.
Bayanan shi na ishara da bukatar shugabannin siyasa da na INEC su fahimci cewa jama’a na fargaba, kuma akwai bukatar yin adalci don ceto kasar daga rikicin bayan zabe.

Source: Twitter
Shirin zabe a rana daya ya jawo martani
Majalisar wakilai na shirin sauya tsarin dokar zabe ta yadda za a rika yin zaben shugaban kasa, na ‘yan majalisar dattawa, wakilai, gwamnoni da na majalisun jihohi a rana guda.
Mai magana da yawun NNPP na kasa, Ladipo Johnson ya ce hakan zai rage kudin da ake kashewa a zabuka da kuma saukaka wa jam’iyyun siyasa gudanar da shirye-shiryensu.
A cewarsa:
“Kudin gudanar da zabe da gwamnati ke kashewa ya yi yawa. Ko da jam’iyyun siyasa ma, zai fi musu sauki da inganci su yi zabensu a rana guda.”
Punch ta wallafa cewa LP ta nuna goyon baya ga wannan shiri, inda kakakinta na kasa, Obiora Ifoh, ya ce hakan yana da amfani.
A nata bangaren, jam’iyyar ADC ta bayyana cewa tana goyon bayan zabuka a rana daya, amma da sharadin cewa INEC za ta inganta tsarin aikinta kafin lokacin.
2027: Hakeem Baba Ahmed ya gargadi Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Dr Hakeem Baba Ahmed ya gargadi shugaba Bola Ahmed Tinubu game da zabe mai zuwa na 2027.
Dr. Hakeem da ya yi murabus daga gwamnatin Bola Tinubu ya ce 'yan Najeriya za su iya kin zaben APC matukar ba a cika musu alkawari ba.
Ya bukaci shugaba Tinubu ya mayar da hankali wajen yin ayyuka na kwarai maimakon mayar da hankali kan siyasa da zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

