Noma: Hadimin Buhari Ya Goyi Bayan Tinubu, Ya Fadi Kuskuren da Aka Samu a Zamaninsu
- Tsohon hadimi a gwamnatin marigayi shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana yadda jama'a suka jahilci shiri gwamnatinsu a kan noma
- Bashir Ahmad ya bayyana haka ne a matsayin martani ga yadda ake neman gwamnati ta yi rangwame a kayan noma a maimakon rage haraji
- Ya ce akwai mutane da dama da suka amfana da shirin noma, amma suka ci amanar gwamnati da talakawan kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Bashir Ahmad, tsohon mataimakin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin sadarwa, ya fadi yadda aka lalata wasu daga cikin shirin tallafin noma a gwamnatinsu.
A cewarsa, yawancin shirye-shiryen tallafi da gwamnatin ta gabatar don amfanin manoma bai haifar da abin da ake bukata ba saboda jama'a sun karkatar da tallafin.

Source: Facebook
Ya wallafa haka ne a shafinsa na X, a matsayin martani ga wani sako da Yakubu Wudil ya wallafa, na sukar matakin gwamnatin tarayya na rangwamen haraji wajen shigo da abinci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin Bashir kan caccakar dabarar Tinubu
A sakonsa a shafin X, Wudil ya ce zai fi amfani a rage farashin takin zamani, tallafa wa manoma da saukin man fetur, da samar da kayan aikin noma na zamani maimakon rangwamen haraji.
Bashir Ahmad ya mayar da martani yana cewa yawancin abubuwan da Wudil ya lissafa an samar da su a zamanin Buhari, musamman ta hanyar Shirin Anchor Borrowers (ABP) da aka fara tun a shekarar 2015.
A cewarsa:
“Wasu daga cikin manoma sun karɓi lamuni har na biliyoyin Naira — wasu har N6bn, amma maimakon su saka a harkar noma, sun karkatar da kudin zuwa sassa kamar mai da iskar gas, canjin kudi da sauransu."

Kara karanta wannan
Gwamnonin 1999 sun nemi Tinubu ya ajiye raba tallafi, ya samar da ayyuka ga matasa
“Wadanda suka yi noma kuwa, bayan sun girbe amfanin gonarsu sai suka boye su, suna jiran su yi tsada, don su samu riba mai yawa, suna cutar da talakawa da aka tsara shirin domin su.”
Bashir ya magantu a kan rufe iyakokin kasa
Dangane da matakin rufe iyakokin kasar da gwamnatin Buhari ta dauka, Ahmad ya ce manufar shirin ita ce 'karfafa samar da kayayyaki a cikin gida, sai dai mutane da dama ba su fahimci abin ba.

Source: Facebook
Ya ce:
“An fassara manufar rufe iyakokin ba daidai ba kuma an rika sukar ta duk da akwai alamun nasara. Shigo da shinkafa daga waje ya ragu, kuma dimbin ‘yan Najeriya sun fita daga matsanancin talauci.”
“Abin bakin ciki shi ne, wadanda suka ci gajiyar shirye-shiryen tallafi sun ci amanar gwamnati da al’umma. Maimakon su taimaka wajen daidaita farashin kayan abinci, sai suka kafa kungiyoyin. suka rika sarrafa kayayyaki da kirkirar karancin kaya domin samun riba mai yawa.”
Bashir ya magantu kan bashin gwamnatin Buhari
A wani labarin, kun ji cewa Bashir Ahmad, ya karyata ikirarin da Sanata Solomon Adeola ya yi, inda ya ce gwamnatin Buhari ta karɓi bashi har Dala biliyan 400 domin farfado da darajar Naira.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Abba ta dura kan bangaren lafiya, za a gyara asibitoci sama da 200 a faɗin Kano
Ahmad ya nuna cewa Hukumar Kula da Bashi ta Ƙasa (DMO) ta bayyana cewa zuwa watan Mayu na shekarar 2023, jimillar bashin da ake bin Najeriya gaba ɗaya ya tsaya ne a dala biliyan 108.3.
Ahmad ya ƙara da cewa daga shekarar 2015, lokacin da Buhari ya hau mulki, zuwa shekarar 2023 da ya sauka, jimillar ƙarin bashi da Najeriya ta ci ƙarƙashin mulkinsa bai wuce Dala biliyan 44.5 ba.
Asali: Legit.ng
