'Yan Bindiga Sun Tare Hanya, An Yi Awon Gaba da Daliban Kwaleji

'Yan Bindiga Sun Tare Hanya, An Yi Awon Gaba da Daliban Kwaleji

  • 'Yan bindiga sun yi aika-aika a jihar Delta bayan sun yi awon gaba da wasu dalibai mata masu yin karatu a wata kwalejin ilmi
  • Miyagun sun sace daliban ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Asaba, babban birnin jihar Delta domin yin wasu abubuwa
  • Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an sako daya daga cikin matan da aka sace bayan da aka biya miliyoyim kudi a matsayin kudin fansa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - 'Yan bindiga sun sace ɗalibai biyu mata na Kwalejin Kimiyya ta jihar Delta.

'Yan bindigan sun sace daliban ne a kwalejin wacce ta ke a Ogwashi-Uku, a ƙaramar hukumar Aniocha ta Kudu a jihar Delta lokacin da suke tafiya a mota.

'Yan bindiga sun sace dalibai a Delta
'Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai a Neja Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa daliban aka sace suna karatu ne a sashen binciken kimiyya na kwalejin.

Kara karanta wannan

'Yan Zamfara sun huro wuta, suna so Dauda Lawal ya sauka daga kujerar gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun sace dalibai a Delta

Wasu majiyoyi daga jama'a sun bayyana cewa an sace su ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida zuwa birnin Asaba cikin wata motar Toyota saloon, a ranar Juma’a, 25 ga watan Yulin 2025.

An dai sace su ne bayan wasu 'yan bindiga sun shiga gabansu da karfi da yaji sannan suka tilasta musu tsayawa kafin su yi awon gaba da su.

"A lokacin da lamarin ya faru, Daya daga cikin matan ne ke tuka motar. Matar aure ce, kuma tana taimakawa abokiyar karatunta ne zuwa Asaba."
"Lamarin ya faru ne a kan titin Polytechnic-Azagba da misalin karfe 6:45 na yamma."

- Wata majiya.

An ce 'yan bindigar sun sako matar auren a ranar Lahadi, bayan karɓar kudin fansa kimanin N10m amma har yanzu ɗaliba ta biyu tana hannun masu garkuwa da mutane har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Babu sauki: Dakarun sojoji sun hallaka 'yan bindiga masu yawa a Neja

An kuma bayyana cewa motar da aka sace su da ita na ajiye ne yanzu haka a ofishin ‘yan sanda na Ogwa-Ukwu.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar Delta, Bright Edafe, ya ce bai ji labarin lamarin ba a lokacin da aka nemi jin ta bakinsa.

"Ban da masaniya kan wannan lamarin."

- Bright Edafe

'Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai a Neja
'Yan bindiga sun sace daliban kwaleji a Delta Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya tare da jami'an rundunar 'Hybrid Forces' sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga masu yawa a jihar Neja.

Sojojin sun samu nasarar ne bayan sun tare 'yan bindigan a lokacin da suke kokarin kai hari a wani kauye da ke karamar hukumar Shiroro.

Nasarar sojojin ta samu ne bayan jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun ba su bayanan sirri kan motsin 'yan bindiga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng