Cakwakiya: Asirin Amarya Ya Tonu, Ƴan Sanda Sun Kama Ta Watanni bayan Ɗaura Aurenta

Cakwakiya: Asirin Amarya Ya Tonu, Ƴan Sanda Sun Kama Ta Watanni bayan Ɗaura Aurenta

  • Ƴan sanda sun kama amaryar a watan Maris, 2025 bisa zargin yin garkuwa da kanta domin biyan bashin N3.6m a jihar Delta
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Delta ya ce an kama amaryar tare da duk waɗanda suka haɗa baki wajen aikata laifin
  • Ya ce matar ta amsa laifinta, ta kuma bayyana yadda suka raba Naira miliyan 3 da suka karɓa a matsayin kudin fansa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta - Wata Amarya ƴar shekara 29 ta ƙirƙiri labarin sace kanta don karɓar kuɗin fansa da za ta biya bashin Naira miliyan 3.6 da ta aro daga ɗan uwanta a lokacin bikinta.

Amaryar, wacce aka ɗaura aurenta a watan Maris, 2025 ta shirya labarin garkuwa da kanta domin ta biya bashin da ta ƙarɓa a jihar Delta.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Jami'an sojoji, ƴan sanda da dakarun CWC sama da 130 sun 'mutu' a Katsina

Yan sanda sun kama amarya a Delta.
Amarya ta yi garkuwa da kanta, ta karbi kudin fansa don ta biya bashi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta cafke amaryar mai suna, Merit Eleh, tare da wasu da ake zargin sun taimaka mata wajen shirya hakan, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amarya ta yi garkuwa da kanta a Delta

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Bright Edafe, ya bayyana cewa sun samu rahoton garkuwa da matar a ranar 21 ga Yuli, 2025, da misalin ƙarfe 8:30 na dare.

Ya ce a rahoton da aka kawo masu, an bayyana cewa wasu 'yan bindiga ne suka sace sabuwar amarya a unguwar Bonsaac, a Asaba, bababan birnin jihar Delta.

A cewarsa, Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Delta, CP Olufemi Abaniwonda, ya umarci dakarun sashin yaƙi da garkuwa da mutane su tabbata sun ceto amaryar cikin ƙoshin lafiya.

Ya umarci kwamandan rundunar ta musamman ta yaƙi da garkuwa da mutane da laifukan yanar gizo, CSP Godwin Osadolor, ya jagoranci binciken don ceto ta.

"Bisa wannan umarni, rundunar ta gudanar da aiki na sirri, inda suka kama wani mutum mai suna Alfred Elisha a shataletalen Koka da kuma wani Ugochukwu Adim a unguwar DLA Road a Asaba, da safiyar 22 ga Yuli, 2025."

Kara karanta wannan

Matashi ya tono gawar kakarsa don ya yi kuɗi, ya tsinci kansa a gagarumar matsala

Yadda asirin amaryar ya tonu bayan ta karɓi N3m

Edafe ya ƙara cewa bayan cafke waɗanda ake zargi, ɗaya daga cikinsu ya amsa cewa ba a yi garkuwa da matar ba, illa dai sun haɗa baki ne da ita don karɓar kuɗin fansa.

Bayan bayyanar gaskiyar lamarin, rundunar ta kama Merit Eleh, wadda ta amsa cewa ɗan uwanta take son ta biya bashin Naira miliyan 3.6 wanda ya taimaka mata da shi wajen shirya bikin aurenta.

An kama amaryar da ta sace kanta.
Yadda asirin amaryar da ta sace kanta ya tonu a Delta Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kakakin ƴan sandan ya ce amaryar ta ce ta yi amfani da kudin wajen shirya shagalin 'Bridal Shower' da biyan kudin ɗakunan otal a lokacin bikinta, inji Punch.

"Ta amsa cewa bayan ta yi garkuwa da kanta, ta karɓi Naira miliyan 3, ta bai wa waɗanda suka taimaka mata N500,000 daga ciki."

Hadiza Mamuda ta kashe mijinta a Yobe

A wani labarin, kun ji cewa ƴan sanda sun damƙe wata mata, Hadiza Mamuda bisa zargin kashe maigidanta kan abinci a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Yobe: Wata mata, Hadiza Mamuda ta kashe mijinta kan abin da yake kawo mata kullum

An ruwaito cewa matar ta zama ajalin mijin ne sakamakon saɓanin da ya shiga tsakaninsu har suka yi faɗa da doke-doke.

Wannan mummunan al'amari ya faru ne a ƙauyen Garin Abba da ke yankin ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe ta Arewa maso Gabas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262