Rashin Tsaro: Jami'an Sojoji, Ƴan Sanda da Dakarun CWC Sama da 130 Sun Mutu a Katsina

Rashin Tsaro: Jami'an Sojoji, Ƴan Sanda da Dakarun CWC Sama da 130 Sun Mutu a Katsina

  • Gwamnatin Katsina ta ce jami'an tsaro sama da 130 sun rasa rayukansu a yaƙi da matsalar tsaro daga watan Mayu, 2023 zuwa yau
  • Kwamishinan tsaro, Dr. Nasir Mu'azu ya ce jami'an tsaron da suka mutu sun haɗa da dakarun CWC na gwamnatin jiha su 100 da sojoji da ƴan sanda akalla 30
  • Ya nuna damuwa kan yadda ake yaɗa rahotanni ƙarya game da yanayin tsaron jihar Katsina, yana mai cewa an samu sauƙi sosai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Gwamnatin Katsina ta tabbatar da mutuwar akalla dakarun rundunar ƴan sa-kai na CWC 100 da sojoji da ƴan sanda sama da 30 a yaƙi da matsalar tsaro a jihar.

Gwamnatin ta bayyana cewa jami'an tsaron sun rasa rayukansu ne a bakin aiki yayin da suke ƙoƙarin kare al'umma daga hare-haren ƴan bindiga daga 2023 zuwa yau.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Dakarun Sojoji sun hallaka ƴan bindiga sama da 3,000 a jihohin Arewa

An kashe jami'an tsaro 130 a Katsina.
Gwamnatin Katsina ta ce an samu nasara sosai a yaki da ƴan bindiga Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida na jihar, Dr. Nasir Mu’azu, ne ya bayyana hakan domin ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa a soshiyal midiya, cewar rahoton Daily Trust.

Da gaske matsalar tsaro ta munana a Katsina?

Dr. Nasir ya bayyana rahotannin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta game da taɓarɓarewar tsaro a Katsina a matsayin ƙarya da ƙoƙarin firgita jama'a.

Ya ce:

"Gwamnatin Jihar Katsina ta nuna damuwa kan yadda wasu ke ƙoƙarin haifar da firgici a tsakanin al’umma ta hanyar yaɗa labaran ƙarya da ke ɓoye gaskiya a kafafen sada zumunta.”

Sannan Dr. Nasir Mu’azu ya ce waɗannan ƙarerayi na ƙoƙarin ɓoye ci gaban da aka samu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da matsalolin tsaro tun bayan hawan Gwamna Dikko Umaru Radda mulki.

An samu sauƙin matsalar tsaro a Katsina

A cewarsa, lokacin da Gwamna Dikko Radda ya hau kujerar mulki a shekarar 2023, kananan hukumomi 24 cikin jihar suna fama da matsalar ’yan fashin daji.

Kara karanta wannan

"Lokaci ya yi" Gwamnatin Tinubu ta yiwa ƴan bindiga 'tayi' a Arewacin Najeriya

Sai dai ya ce, “ta hanyar dabaru da tsare-tsare masu inganci da haɗin kai da hukumomin tsaro, an samu gagarumin ci gaba a yawancin sassan jihar.”

Kwamishinan ya ce yanzu kananan hukumomi 11 da suka haɗa da Jibia, Batsari, Danmusa, Katsina, Batagarawa, Charanchi, Bindawa, Ingawa, Kafur, Danja da Kusada sun samu zaman lafiya.

Har wa yau, ya ce an samu sauƙin hare-hare sosai kananan hukumomi tara da suka haɗa da Malumfashi, Kurfi, Dutsinma, Kankia, Musawa, Bakori, Funtua, Sabuwa da Dandume.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
Gwamnatin Katsina ta ce za ta ci gaba da ɗaukar matakan dawo da zaman lafiya a faɗin jihar Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Gwamnatin Katsina na ƙoƙarin dawo da tsaro

Dr. Nasir ya bayyana cewa sauran kananan hukumomi huɗu da har yanzu ake fama da hare-haren ’yan ta’adda su ne, Faskari, Kankara, Safana da Matazu.

“Duk da ƙalubalen da ake fuskanta a wasu ƙananan hukumomi, gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a guiwa ba. Gwamna Radda yana da ƙwarin gwiwa da cikakken ƙuduri na dawo da zaman lafiya da doka da oda," in ji shi.

- Dr. Nasir Mu'azu.

Wani ɗan yankin ƙaramar hukumar Ɗanja, Abdullahi Yahuza ya shaidawa Legit Hausa cewa a zahirin gaskiya an samu sauƙi fiye da shekarun baya.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya yi fatali da tsarin jam'iyya mai mulki, ya yi barazanar sauya sheƙa

"A da, su kan shigo nan su ɗauki wanda suka ga dama su yi garkuwa da shi, amma tun da aka kafa C-Warch komai ya yi sauƙi da taimakon Allah," in ji shi.

Sai dai wani ɗan garin Guga a ƙaramar hukumar Bakori ta Katsina ya ce kullum hare-haren ƴan bindiga ƙaruwa yake a yankinsu.

Ya yi kira ga gwamnatin Katsina da ta ƙara dagewa wajen magance wannan matsala, yana mai cewa ƴan uwa da abokansa da dama sun bar mahaifarsu.

Ƴan bindiga sun kai hari jihar Katsina

A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun tafka ɓarna yayin da suka kai hari a ƙauyen Unguwar Gada da ke ƙaramar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Maharan sun yi nasarar sace dabbobi da ba a bayyana adadinsu ba, tare da jikkata wasu mazauna ƙauyen mutum biyu a harin na ranar Juma'a.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun yiwa jami'an tsaro kwantan ɓauna lokacin da suka kai wa jama'ar garin ɗauki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262