Hadimin Tinubu Ya Hango Kuskuren da Kwankwaso Ya Yi a Kalamansa kan Arewa

Hadimin Tinubu Ya Hango Kuskuren da Kwankwaso Ya Yi a Kalamansa kan Arewa

  • Ana ci gaba da mayar da martani ga jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso kan zargin da ya yi cewa gwamnatin Bola Tinubu ta yi watsi da Arewa
  • Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin jaridu, Abdulaziz Abdulaziz ya ce zargin da Rabiu Kwankwaso ya yi ba gaskiya ba ne
  • Ya ce gwamnatin Bola Tinubu na aikin tituna ne a matakin kasa kuma babu wani yanki da take nuna wa wariya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hadimin Shugaban Ƙasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce gwamnatin Bola Tinubu na aiwatar da ayyukan tituna a faɗin ƙasar nan ba tare da nuna wariya ga kowane yanki ba.

Abdulaziz, wanda shi ne mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin jaridu, ya ce gwamnati na ayyuka a wuraren da ƴan Najeriya za su amfana.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake magana kan 'haduwar' Tinubu da Kwankwaso

Abdulaziz Abdulaziz da Shugaba Tinubu.
Hadimin shugaban ƙasa, Abdulaziz Abdulaziz ya musanta kalaman Kwankwaso Hoto: Abdulaziz Abdulaziz
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin The Morning Brief na Channels tv a ranar Litinin, 28 ga watan Yuli, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya jefawa gwamnatin Tinubu zargi

Hadimin shugaban ƙasa ya yi wannan bayani ne a matsayin martani ga jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso, wanda ya yi zargin cewa Tinubu ya yi watsi da Arewa.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Kwankwaso ya ce gwamnatin Tinubu tana karkatar da albarkatun ƙasa mafi tsoka zuwa yankin Kudu.

Daga cikin zargin da Kwankwaso ya yi, ya ce gwamnati mai ci ta manta da titin Abuja zuwa Kano, inda ya bayyana yadda ya sha wahala da ya biyo hanyar a mota.

Hadimin Tinubu ya maida martani

Sai dai Abdulaziz ya ce idan aka duba za a ga dukkan ayyukan da gwamnatin Tinubu ke yi na ƙasa ne, inda ya jaddada cewa gwamnatin ba ta nuna wariya ga kowane yanki ba.

Kara karanta wannan

Sukar gwamnati: Jam'iyyar NNPP ta ba Tinubu shawara kan Kwankwaso

A cewarsa:

"Ya kamata mu kalli waɗannan ayyuka a matsayin ayyukan ƙasa, ba wai na Arewa ko Kudu ba, wanda shi ne babbar matsala.
"Abu mafi muhimmanci shi ne wane amfani waɗannan ayyuka ke da shi, ba wai saboda an gina su a Arewa ko Kudu ba. Wane ƙofofin bunƙasar tattalin arziki titunan za su buɗe.
"Tabbas, akwai buƙatar adalci da daidaito, kuma ina da tabbacin cewa babu wanda zai iya zargin wannan gwamnati da nuna wariya ko rashin adalci ga Arewa ko Kudu, domin tana ayyuka daidai gwargwado a kowane yanki.”
Shugaba Bola Tinubu da Kwankwaso.
Hadimin Tinubu ya ce an ci gaba da aikin titin Abuja zuwa Kano Hoto: @OfficialABAT, @kwankwasoRM
Source: Facebook

Gwamnatin Tinubu ta jingine titin Abuja-Kano?

Har wa yau, Abdulaziz ya musanta zargin da Kwankwaso ya yi cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da aikin titin Abuja-Kaduna-Kano inji rahoton Daily Post.

Ya ce tuni aiki ya kankama a titin, wanda ke da matuƙar muhimmanci wajen haɗa Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar nan.

Ya kuma ce babban titin Sokoto zuwa Badagry da ake yi yanzu ya shafi Arewa, kuma yana daidai da titin gabar teku daga Legas zuwa Calabar da ke kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Minista ya soki Kwankwaso da ya taba Tinubu, ya masa gorin ƙuri'un Buhari miliyan 12

Kwankwaso zai haɗe da Shugaba Tinubu?

A wani labarin, kun ji cewa Abdulaziz Abdulaziz ya nuna alamun cewa wataƙila Rabiu Kwankwaso da Bola Tinubu su sake haɗewa a inuwa ɗaya.

Hadimin shugaban ƙasar ya ce siyasa ce ke kawo haɗin kai da rabuwa kai a wasu lokutan amma dama tun da daɗewa akwai abokantaka tsakanin Shugaba Tinubu da Kwankwaso.

A cewarsa, Tinubu da Kwankwaso sun dade suna hulɗa da juna tun kafin su zama gwamnoni a 1999, domin sun fara siyasa tare a 1993.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262