Asiri Ya Tonu: An Kama Bindigogi ana Kokarin kai Su Kano daga Filato
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce ta cafke wasu mutane da ake zargi da safarar makamai zuwa Kano a karamar hukumar Kazaure
- An kuma gano mota da aka sace daga kasuwar Gujungu a ƙaramar hukumar Taura a ƙoƙarin ficewa da ita zuwa Jamhuriyar Nijar
- Wasu da ake zargi da yanke wayoyin lantarki sun shiga hannu a Ringim tare da kama motar da suka yi amfani da ita wajen satar kayan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa – Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta samu gagarumar nasara a fafutukar da take yi na yakar masu aikata laifuffuka a fadin jihar, inda ta cafke masu safarar makamai.
An kama wasu mutane da ake zargin za su shiga Kano da bindigogin da suka taho da su daga Jos na jihar Filato.

Source: Facebook
Kakakin rundunar SP Shiisu Lawan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Facebook a ranar 27 ga watan Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama masu safarar makami zuwa Kano
A ranar 8 ga watan Yuli, 2025, rundunar ta sanar da kama Abdussamad Haruna, ɗan shekara 30 daga ƙauyen Dansure kusa da Gwiwa, yayin da yake ƙoƙarin safarar bindiga zuwa Kano.
A cewar ‘yan sandan jihar Jigawa, an same shi da bindigar aka ɓoye a cikin buhu yana kokarin shiga Kano da ita.
Bayan haka kuma, a ranar 20 ga Yuli, an cafke wani matashi mai suna Auwalu Yusuf, ɗan shekara 24 daga Kofar Wambai, Kano, wanda shi ma aka samu da wata bindiga a hannunsa.
Bincike ya nuna cewa suna da alaka da wani mai safarar makamai daga Barikin Ladi, jihar Filato, da ke da alaƙa da miyagun ƙungiyoyi a Kano da Jigawa.

Source: Facebook
An kama motar da aka sace a Jigawa
Rundunar ta bayyana cewa ta gano wata mota kirar Kia Sorento mai lamba GWL 225 BB da aka sace daga kasuwar Gujungu a karamar hukumar Taura a ranar 14 ga Yuli, 2025.
An bayyana cewa wasu miyagun mutane ne suka yi amfani da cunkoson kasuwa wajen satar motar.
Amma bayan korafi, ‘yan sanda daga sashen Gujungu sun bi sahun motar har zuwa ƙauyen Kanya Babba a Babura, inda suka samo ta.
Rahotanni sun bayyana cewa masu laifin sun tsere, amma an dawo da motar bayan tantance ainihin mai ita.
An cafko barawon kayan lantarki a Ringim
A Ringim kuma, ‘yan sanda sun cafke wani matashi mai suna Abubakar Sadi, ɗan shekara 25 daga Kofar Waika, Kano, bisa zargin yanke wayoyin lantarki daga na’urorin gwamnati.
An kama shi ne a cikin wata mota da ke cike da wayoyin wutar lantarki da aka sace daga yankin, yayin da sauran mutane huɗu suka tsere.
Yadda aka sha kama kayan barna a Arewa
A Najeriya, samun makamai a hannun masu laifi ya zama ruwan dare, kuma hukumomin tsaro na ci gaba da yin nasarori a kokarinsu na kama irin wadannan miyagu.
A duk fadin kasar, musamman a Arewacin Najeriya, an sha cafke mutane da makamai irin su bindigogi, harsasai, da kayan yaki, wadanda ake kokarin safararsu ta ɓoyayyen hanya zuwa manyan birane kamar Kano, Kaduna, da Sokoto.
Jihar Kano, kasancewarta cibiyar hada-hadar kasuwanci da yawan jama’a, na daya daga cikin wuraren da ake yawan kai makamai, inda ake zargin suna shigowa daga jihohi kamar Zamfara, Katsina, da Filato.
A lokuta da dama, rundunar ‘yan sanda ta kama motocin da ke ɗauke da bindigogi da harsasai da aka ɓoye a cikin buhu, taya ko kofofin mota, domin kauce wa binciken jami’an tsaro.
Hakanan, rahotanni sun nuna cewa akwai hanyoyi na musamman da ake bi daga yankunan da ke fama da rikici don kai makamai zuwa Kano, inda ake zargin suna shiga hannun kungiyoyin ‘yan fashi da masu aikata ta’addanci.
Hukumomi na kara tsaurara matakai, amma matsalar na ci gaba da zama babbar barazana ga tsaron kasa.
'Yan sanda sun kama sojoji a jihar Ogun
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta sanar da cafke wasu mutane 22 a wani otel.
Cikin mutanen da aka samu nasarar cafkewa akwai sojoji biyu da wasu mata da ake zargi suna da alaka da wata kungiyar asiri.
Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan kungiyar asiri ne suka shirya taro a otel din ba bisa ka'ida ba kafin a kai musu farmaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



