Kano: An Ɗauki Mataki a kan Dabbobin Dawan gidan Tsohon Akanta bayan Mesa ta Tsere

Kano: An Ɗauki Mataki a kan Dabbobin Dawan gidan Tsohon Akanta bayan Mesa ta Tsere

  • Jami'ai a Kano sun kamo mesar da ta tsere daga gidan tsohon Akanta Janar na ƙasa, Ahmed Idris a jihar Kano
  • Shugaban kula da gidan namun daji a jihar, Sadik Kura Muhammad ne ya tabbatar da hakan bayan jama'a sun yi ƙorafi
  • Ya ce an gano mesar amma duk da haka, tsohon Akanta Janar bai karya wata doka ba don ya yi kiwon namun daji a gidansa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugaban gidan namun daji a jihar Kano, Sadik Kura Muhammad, ya yi karin bayani kan halin da ake ciki bayan Mesa ta tsere daga gidan tsohon Akanta Janar, Ahmed Idris.

Tserewar macijin, wanda aka bayyana da cewa Mesa ce, ya jefa fargaba a tsakanin mazauna unguwar Daneji da kewaye a jihar Kano a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Dattawa sun faɗi dalilan da suka jawo Arewa ta tsaya cak, babu cigaba a Najeriya

Tsohon Akanta Janar ya yi kiwon dabbobi a Kano
An gano mesar da ta gudu daga gidan tsohon Akanta janar a Kano Hoto: Akeem Rahman/Ontario Parks NE
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Sadik Kura Muhammad ya tabbatar da cewa sauran namun dawa da aka samu a gidan tsohon Akanta sun haɗa da kada da kuma ɗan damisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An maida su gidan dabbobi a Kano

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Sadik Kura Muhammad ya ce an kamo mesar da ta tsere daga gidan tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris a Kano.

Ya kara da cewa an kuma kwashe dukkannin namun daji da aka samu a gidansa zuwa gidan adana namun daji na jihar.

Mazauna unguwannin Daneji, Mandawari, Kabara da Soron Dinki sun bayyana cewa sun gaza samun sukuni tun bayan ɓullar labarin ajiye namun daji a gidan tsohon Akantan.

Sai dai shugaban gidan Zoo a Kano ya ce tsohon Akanta Janar ya yanke shawarar mika namun dajin ga hukumomi da kansa, kuma yanzu duka suna karkashin kulawarsu.

'Tsohon Akanta zai iya kiwon namun daji a gida'

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kai farmaki a Neja, an yi awon gaba da bayin Allah

Sadik ya bayyana cewa Ahmed Idris yana da cikakken lasisi na kiwon namun daji, kuma dabbobin da ke gidan nasa ba su kai matsayin barazana ga rayuwa ba.

Tsohon Akanta Janar ya miƙa namun daji ga gidan zoo
Gwamnati ta ce tsohon Akanta Janar na da lasisin kiwon namun dawa Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewarsa:

“Akwai wata doka a kan namun dawa, wacce ke ba mutane damar kiwon wasu namun daji a gidajensu. Amma nau’ukan da ke gab da karewa, kamar tsuntsayen aku da gaggafa, dole a yi kiwonsu a gidan zoo domin kare jinsinsu."

Ya ce saboda ƙorafe-ƙorafen da maƙwabta suka yi, Ahmed Idris da kansa ya yanke shawarar mika dabbobin ga gwamnati.

“Mun kwashe dabbobin da daddare domin kaucewa tsoro ko ruɗani."

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa an fara bincike, kuma an gayyaci tsohon Akanta Janar don yi masa tambayoyi game da batun.

Yadda masu hannu da shuni ke ajiye dabbobi a gidajensu

A Najeriya, musamman a tsakanin masu hannu da shuni, yana kara zama ruwan dare ganin wasu na kiwon namun daji masu ban mamaki a cikin gidajensu.

Wadannan dabbobi na iya hada da damisa, kada, birai, ko kuma namun da ba a saba gani a cikin gida ba kamar mesa — irin wanda ya tsere daga gidan tsohon Akanta Janar, Ahmed Idris, a Kano.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke budurwar da ta kashe yara 2, an ceto jariri

Wadanda ke da wadatar dukiya na yin hakan domin nuna matsayi, ko kuma sha'awa ta musamman ga dabbobi.

Sai dai hakan na iya haifar da matsaloli ga makwabta da ma al’umma baki daya. Tserewar dabba mai hatsari na iya jefa jama’a cikin firgici da fargaba, kamar yadda ya faru a Kano, inda mazauna unguwa suka rasa sukuni bayan mesar ta tsere.

Baya ga hadarin da dabbobin ke haifarwa, akwai kuma batun rashin tsaro da kariya da ya kamata a kiyaye.

Duk da cewa akwai dokokin kiwon namun daji a gida, ba kowa ne ke bin ka’ida ba, kuma ba kowane yanki ne ke da isasshen iko ko kayan aiki don sa ido ba.

Don haka, yana da matukar muhimmanci hukumomi su kara sa ido da wayar da kai game da wannan dabi’a da ke iya zama barazana ga zaman lafiya a cikin gari.

Batan mesa ya gigita mazauna Kano

A baya, mun ruwaito cewa jama'a sun shiga firgici a jihar Kano bayan tabbacin batan wata mesa daga gidan tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta dura kan bangaren lafiya, za a gyara asibitoci sama da 200 a faɗin Kano

Rahotanni sun ce macijin ya kubce daga gidan Idris da ke unguwar Daneji, lamarin da ya tayar da hankula a tsakanin mazauna unguwar da kewaye.

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya nuna matuƙar damuwa dangane da faruwar lamarin, inda ya bukaci rundunar ƴan sandan jihar ta bincika lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng