Bello Yabo Ya Yi Zazzaga kan Batun Yafewa Marigayi Buhari bayan Ya Rasu

Bello Yabo Ya Yi Zazzaga kan Batun Yafewa Marigayi Buhari bayan Ya Rasu

  • Sheikh Bello Aliyu Yabo ya shawarci masu mulki su tuba kafin mutuwa, yana sukar wadanda ke neman a yafe wa Muhammadu Buhari
  • Ya ce rashin mayar da dukiyar da aka wawure da kuma karancin nadama yana nuna cewa zalunci da cin hanci an yi su da gangan ne
  • Malamin ya koka kan yadda 'yan Najeriya ke yafewa duk da halin kunci, yana cewa Allah ma yana da sharudda kafin yafewa mai zalunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Sheikh Bello Aliyu Yabo ya ja hankalin al'umma kan tuba kafin lokaci ya kure musamman masu mulki.

Sheikh Yabo yana magana ne game ce-ce-ku-ce da ake ta game da yafewa marigayi Muhammadu Buhari.

Bello Yabo ya magantu bayan rasuwar Buhari
Bello Yabo ya yi magana kan batun yafewa marigayi Buhari. Hoto: Sheikh Bello Aliyu Yabo.
Source: Facebook

Bello Yabo ya koka kan zaluncin shugabanni

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

'Yadda matata ta hana ni sukar Buhari bayan ya mutu': Tsohon gwamna ya magantu

A cikin bidiyon, Bello Yabo ya ce ta yaya wasu malamai za su yi amfani da hadisi cewa ko ba ka yafe ba Allah zai tafe masa.

Ya ce abin takaici ne kana ganin wadanda suka kwashe muku dukiya suna facaka amma ace a yafe musu.

A cewarsa:

"Abin da yake faruwa kwanakin nan, wasu malamai sun yi amfani da wannan hadisin.
"Cewa ko ba ku yafe ba ai Allah na iya yafe masa, sai dai waɗanda ake magana a kansu har suka mutu ba su mayar da abin da suka dauka ba.
"Da su da wadanda suka daure wa gindi suka kwashe mana dukiya ba su dawo da ita ba, sai mu da aka maida wawaye a ce ku yafe."
Bello Yabo ya shawarci shugabanni bayan rasuwar Buhari
Bello Yabo ya fadi ra'ayinsa game da yafewa Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari, Sheikh Bello Aliyu Yabo.
Source: UGC

Sakarcin yan Najeriya da Bello Yabo ke gani

Malamin ya bayyana cewa an mayar da yan Najeriya sakarkaru sai an gama cutarsu a zo ana cewa ku yafe.

Kara karanta wannan

Dukan Islamiyya ya jawo babbar matsala, fitaccen ɗan TikTok ya bar addinin Musulunci

"Saboda mu yan Najeriya sarakunan wauta ga dukiyar mu muna gani su da yayansu suna wadaka mu kuma muna cin garin kwaki, mun yafe, mun yafe.
"Ta yaya za ka yi zalunci mutane sama da miliyan 200 gabanka bai fadi ba lokacin da kake zalunci.
"Kuma zaluncin ba kwana guda ba shekara guda ka yi shekaru takwas kana zaluntar mutane."

- Cewar Sheikh Yabo

Sheikh Yabo ta ce abin bakin ciki ne yadda aka yi zalunci da gangan tsawon shekaru takwas ba tare da nadama ba sai da mutuwa ta zo.

Ya kara da cewa:

"Kuma zaluncin nan ba ka yi shi ba ne bisa kuskure ba da gangan ne saboda idan baka sani ba mutane da yawa sun jawo hankalinka.
"To sai da ka ga uwar bari za ka mutu a ce a yafe mana, in dai ga gaske ai tuba tana da sharudanta."

Yadda jama’a ke cece-kuce kan yafewa Buhari

Bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ce-ce-ku-ce ya barke a kafafen sada zumunta da tsakanin malamai kan batun yafiya da gafara.

Kara karanta wannan

'Dan Bello ya zafafa harshe kan Kwankwaso, ya fara rikici da 'yan Kwankwasiyya

Wasu ‘yan Najeriya da malamai sun bukaci a yafe masa, suna cewa ya rasu ne a matsayin Musulmi, kuma yana da hakkin neman rahamar Allah.

Wasu kuwa na ganin hakan sakaci ne da tarihinsa na mulki da wahalhalun da al'umma suka fuskanta a zamaninsa.

Sheikh Bello Aliyu Yabo na daga cikin wadanda suka fito karara suka soki irin wannan kiran. A cewarsa, ba a yi laifin ne bisa kuskure ba, illa ta gangan aka tafka zalunci da cin hanci cikin shekaru takwas.

Ya koka da yadda wasu malamai ke jaddada cewa Allah zai iya gafarta masa, duk da cewa ba a ga nadama ko mayar da dukiyar kasa da aka ce an wawure ba.

Jama’a da dama na kokawa cewa ba a kamata a rika cewa “ku yafe” yayin da wadanda suka wahala suke rayuwa cikin kunci.

A gefe guda, wasu na ganin tun bayan mutuwa ya kamata a daina magana kan laifi, a bar Allah Ya yi hukunci. Amma ra’ayoyin sun ci gaba da rarraba zukata a kasa.

An gano Bello Yabo da bindiga

Kara karanta wannan

Ana rade radin gwamnan Yobe zai fita daga APC zuwa ADC, hadiminsa ya yi magana

Kun ji cewa Sheikh Muhammad Bello Yabo ya janyo cece-kuce bayan bullar wani bidiyo da aka ga malamin yana wa’azin addinin rike da bindiga.

Malamin ya ce idan har yana rike da bindiga, to babu wani bata gari da zai iya firgita shi, yana mai cewa a shirye yake ya kare kansa.

Yayin da wasu ke goyon bayan matakin malamin na kare kansa daga 'yan bindiga, wasu na ganin hakan zai iya tayar da zaune tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.