Yan Bindiga Sun Saɓa Alƙawari, Sun Yanka Mutum 38 bayan Dafe Miliyoyin Kuɗin Fansa

Yan Bindiga Sun Saɓa Alƙawari, Sun Yanka Mutum 38 bayan Dafe Miliyoyin Kuɗin Fansa

  • Yan bindiga sun kashe wasu daga cikin mutane fiye da 50 da suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya
  • An tabbatar cewa sun hallaka mutum 38 daga cikin waɗanda suka sace a kauyen Banga da ke Kaura Namoda, duk da an biya fansa
  • Aminu Musa Banga ya ce ’yan bindigar sun yanka mutanen bayan karɓar kudin, inda aka saki mutum 18 kawai da suka dawo da rai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Yan bindiga sun saba alkawarin da aka yi da su bayan kisan wasu da suka yi garkuwa da su.

Maharan sun kashe mutum 38 daga cikin 56 da suka sace a kauyen Banga da ke Kaura Namoda a jihar Zamfara.

Yan bindiga sun hallaka wadanda suka yi garkuwa da su
Yan bindiga sun kashe mutum 38 bayan dafe miliyoyin kuɗi. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Yan bindiga sun hallaka wasu da suna kama

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kai farmaki a Neja, an yi awon gaba da bayin Allah

Wannan kisan gilla da suka yi ya biyo bayan biyan kudin fansa fiye da N50 da suka bukata wanda aka ba su, cewar Leadership.

Wani mazaunin yankin, Aminu Musa Banga ta tabbatar da cewa an sace mutanen da dama cikin watannin da suka gabata tare da buƙatar fansa N1m kowanne.

Sai dai Banga ya ce daga cikin mutanen da aka sace, 18 ne kawai aka sako da rai, yayin da sauran 38 aka kashe duk da an biya fansar.

Ya ce:

"Waɗannan 'yan bindiga sun kashe maza 38 da mace ɗaya yayin da suke tsare da su. Mun samu wannan labari daga mutum 16 da suka dawo."
"’Yan bindigar sun yanka su ɗaya bayan ɗaya bayan mun biya fansa fiye da Naira miliyan 50."
Yan bindiga sun hallaka wasu da suka sace a Zamfara
Yan bindiga sun hallaka mutum 38 bayan karbar kuɗin fansa. Hoto: Legit.
Source: Original

An caccaki gwamnati game da rashin tsaro

Banga ya bayyana cewa yankin yanzu yana ƙarƙashin ikon 'yan bindigar, inda ya ce an bar wasu kauyuka saboda tsananin hare-haren.

Ya roƙi gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara da su aika da sojoji domin hana 'yan bindigar ci gaba da addabar yankin, Sahara Reporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ƴan bindiga sun shiga cikin gona, sun ɗauke malami da wasu mutum 2

Shugaban ƙaramar hukumar Kaura Namoda, Hon. Mannir Mu’azu Haidara, ya tabbatar da lamarin kuma ya ce waɗanda aka sako suna cikin mawuyacin hali.

Ya ce:

“Suna karɓar magani a asibitin Kaura Namoda saboda raunukan da suka samu daga duka da kuma wahala da 'yan bindigar suka jefa su.
“In sha Allah, ba za mu gaji ba wajen ɗaukar matakan da suka dace tare da haɗin gwiwa da jami’an tsaro da gwamnatin jihar."

Kakakin 'yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce ba su da masaniya da lamarin saboda ba a kai musu wani rahoto daga yankin ba.

Ya ce irin wannan lamarin ya kamata al’umma su rika kai rahoto da wuri domin a ɗauki matakin da ya dace cikin lokaci.

Dakarun Sojoji sun ragargaji yan bindiga

A wani labarin, kun ji cewa sojojin haɗin gwiwa na Operation Fansan Yamma sun dakile harin 'yan ta’adda a Neja, inda suka kashe miyagu da dama a artabun.

Dakarun sun kaddamar da harin ne bayan samun bayanan sirri, tare da goyon bayan rundunar sama da kuma kwato makamai.

Duk da wannan nasarar, soja guda ɗaya ya rasa ransa, yayin da rundunar ta sha alwashin ci gaba da yaki da ta’addanci a yankin Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.