Kaduna: Ƴan bindiga Sun Shiga cikin Gona, Sun Ɗauke Malami da Wasu Mutum 2
- Yan bindiga sun kai wani hari yayin da suka sace Fasto da wasu biyu a gonarsu da ke Bauda a Maro
- Lamarin ya faru ne a garin da ke cikin Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya
- Wanda aka sace sun hada da Rabaran Anthony Lamba na ECWA, Christiana Anthony da Danlami Zana, yayin da suke aikin gona a ranar Juma’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Al'ummar wani kauye da ke jihar Kaduna sun shiga tashin hankali bayan wani harin yan bindiga a yankin.
Maharan sun shiga kauyen da ke ƙaramar hukumar Kajuru inda suka sace mutane uku yayin harin.

Source: Facebook
Rahoton Zagazola Makama ya ce yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani Fasto da ke cikin gonarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yan bindiga ke sace al'umma a Arewa
Wannan ba shi ne karon farko ba da yan bindiga ke sace malaman addinin Musulunci har ma da na Kiristanci a yankin Arewacin Najeriya.
An sha samun bayanai kan yadda al'ummomi ke shiga tsaka mai wuya musamman kan hare-haren yan ta'adda wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Bayan satar malaman addini, maharan na shiga har cikin fadar sarakunan gargajiya inda suke sace su da kuma hallaka mutane yayin hare-haren da suke kai wa.

Source: Original
Yan bindiga sun sace basarake a Kaduna
Ko a kwanakin baya ma maharan sun shiga wani kauye a jihar Kaduna inda suka yi barin wuta tare da sauke basarake.
Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace mai unguwar Bauda da ke Maro, karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna da asuba.
Rahoto ya ce 'yan bindigar sun kai farmaki ne da misalin karfe 1:00 na safe, sun tafi da Obadiah Iguda kadai ba tare da kashe kowa ba.
Lamarin ya tada hankalin al'umma, yayin da hukumar Kufana ta bukaci gaggawar daukar matakin tsaro domin hana sake faruwar hakan.
Yadda aka sace Fasto da wasu a gona
Majiyoyi sun shaida cewa an sace Rabaran Anthony Lamba, mai shekara 50 na cocin ECWA Bauda, Christiana Anthony da Danlami Zana.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kama su ne a gonarsu ranar Juma’a 25 ga watan Yulin 2025 da tsakar rana.
Rundunar tsaro ta kai dauki, amma masu garkuwar sun gudu da su zuwa inda ba a sani ba.
An kara kokarin ceto mutanen ba tare da rauni ba, yayin da bincike kan lamarin ke gudana a halin yanzu.
An farmaki Fulani da sace musu shanu a Kaduna
Mun ba ku labarin cewa wasu 'yan fashi dauke da makamai sun kai farmaki kauyen Dutsen Wai da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Wani rahoto ya bayyana cewa maharan sun yi harbi sama don tsorata jama'a, sannan suka kwashe dabbobi da dama.
Rundunar 'yan sanda da sojoji sun fara bincike tare da hadin gwiwar masu sa-kai domin gano inda 'yan fashin suka nufa.
Asali: Legit.ng

