Minista Ya Soki Kwankwaso da Ya Taba Tinubu, Ya Masa Gorin Ƙuri'un Buhari Miliyan 12
- Ministan Ayyuka, David Umahi ya yi magana kan zargin Rabi'u Kwankwaso cewa Bola Tinubu yana fifita Kudu fiye da Arewa
- Umahi ya ce Kwankwaso na kokarin yaudarar ’yan Arewa ne da burin gaje irin farin jinin da Muhammadu Buhari ya samu a yankin
- Umahi ya bayyana jerin manyan ayyuka a yankunan biyu, yana cewa Arewa na da kashi 52% na ayyukan da ake yi yanzu haka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi ya caccaki Sanata Rabiu Kwankwaso kan sukar Bola Tinubu.
Umahi ya ce zargin da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso kan gwamnatin Tinubu ya yi ba gaskiya ba ne.

Source: Facebook
An caccaki Kwankwaso kan sukar Buhari
A wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Umahi ya ce Kwankwaso na yada ƙarya ne domin yaudarar ’yan Arewa da son neman shahara, cewar Vanguard.
Kwankwaso ya zargi gwamnatin Tinubu da fifita Kudu wajen ayyukan raya kasa, abin da Umahi ya kira yaudara da son zuciya.
Ya kuma gargade shi da ka da ya yi mafarkin gadon martabar marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ba da ƙarya ake hakan ba.
Umahi ya ce:
“Kwankwaso ya fadi cewa shugaban kasa Tinubu yana gina tituna a Kudu fiye da Arewa. Wannan ƙarya ne.
“Ina ganin wannan magana ba gaskiya ba ce, kuma Kwankwaso na son ya nuna shi ne mai kaunar Arewa fiye da kowa.
“Ina ganin wannan kalamai ne na shirme da son nuna kamar zai gaji Buhari, amma ba da yaudara ba ake yin hakan.
“Ba za a iya gadon Buhari da kalmomi kawai ba. Wannan aiki ne na shekaru da jajircewa da gaskiya da rikon amana.”
Umahi ya jaddada cewa Buhari ya yi aiki tukuru domin ƙasar nan, kuma ya roki Allah ya saka masa da aljanna.

Source: Getty Images
Kwankwaso: Minista ya jero ayyukan Tinubu a Arewa
Umahi ya ce yana da muhimmanci a sanar da jama’ar Arewa ayyukan da ake yi domin su san gaskiyar lamarin da ba a ɓoye ba, cewar Premium Times.
Ya bayyana wasu daga cikin manyan ayyukan tituna da ake yi a dukkan shiyyoyin ƙasar nan kamar yadda Tinubu ya tsara.
Ministan ya ce manyan ayyukan sune: Titin Lagos-Calabar, Sokoto-Badagry da kuma hanyar Akwanga-Jos-Gombe.
Ayyukan Tinubu sun kai tsawon kilomita 2,722 gaba ɗaya, kuma 52% daga ciki na Arewa ne, 48% kuma na Kudu ne.
Sauran ayyukan Tinubu a Arewacin Najeriya
A titin Sokoto-Badagry, Umahi ya ce ana aikin kilomita 378 a Arewa, wanda ya fi 350 na Kudu, abin da ke nuna gaskiyar lamarin.
Ya soki Kwankwaso da cewa bai yi adalci ba wajen zargin Tinubu da nuna wariya, yayin da Arewa ke da mafi yawan titunan da ake yi.
Ministan ya kuma lissafa wasu ayyuka da ke faruwa a Arewa da suka hada da hanyoyin Abuja-Kano, Sokoto-Zaria, Kano-Maiduguri da sauransu.

Kara karanta wannan
An ja layi tsakanin Kwankwaso da Tinubu, fadar shugaban kasa ta yi wa Madugu raddi
Akwai kuma ayyukan da ke tafiya ta jigawa, Katsina, Kano, Borno, Kebbi da Yobe da dama da ke ci gaba da aiki a bangaren Arewa.
Umahi ya ce duk wadannan ayyuka na nuna cewa Tinubu yana son ci gaban kowane yanki, ba tare da nuna wariya ba.
An bukaci Kwankwaso ya ba Tinubu hakuri
Mun ba ku labarin cewa Ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce babu wata wariya a rabon ayyukan tituna tsakanin Arewa da Kudu a gwamnatin Bola Tinubu.
Ya ce zargin Sanata Rabiu Kwankwaso na cewa Kudu ta fi samun tituna ba gaskiya ba ne, ya kira hakan da yaudara ga mutanen yankin Arewa.
Umahi ya bukaci Kwankwaso da ya janye maganarsa tare da ba Tinubu hakuri yayin da ya ce 'yan Arewa sun fi cin moriyar wasu ayyukan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

