Yadda Aka Mutunta Wasiyyar Marigayi Sarkin Gusau yayin Birne Shi a Zamfara

Yadda Aka Mutunta Wasiyyar Marigayi Sarkin Gusau yayin Birne Shi a Zamfara

  • An birne marigayi Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello a makabartar al'umma bayan gudanar da sallar jana'iza
  • An tabbatar da bin wasiyyarsa ne kamar yadda ya bukata, maimakon biene shi a kaburburan sarakunan gidansu
  • Sarkin Anka, Attahiru Ahmad, ya bayyana cewa marigayin ya kasance mai gaskiya, son jama’a, da rikon amana a mulkinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - A jiya ne aka tabbatar da rasuwar Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello bayan ya sha fama jinya na tsawon lokaci.

An birne marigayi Sarkin Gusau na jihar Zamfara a makabartar jama’a da ke birnin Gusau a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

An birne Sarkin Gusau a makabarta ba gida ba
An birne Sarkin Gusau a makabarta kamar yadda ya buƙata. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan Zamfara, ya bayyana hakan ga Vanguard a yau Asabar 26 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Musulunci ya yi babban rashi, Sheikh Dalha Konduga ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rasuwar Sarkin Gusau ta girgiza al'ummar Najeriya

Legit Hausa ta ruwaito cewa marigayin ya rasu yana da shekara 71 a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja a ranar Juma’a bayan doguwar jinya.

An gudanar da sallar jana’iza a Gusau ranar Juma’a inda dubban mutane suka halarta ciki har da Gwamna Dauda Lawal.

Har ila yau, daga cikin mahalarta jana'izar akwai mataimakinsa, Alhaji Mani Mummuni, da ‘yan majalisa na tarayya da na jiha.

A baya tun shekarar 2016 an taba yada cewa Sarkin Katsinan Gusau, Dr. Ibrahim Bello ya rasu amma daga bisani aka gano ba gaskiya ba ne.

Yaushe marigayi Sarkin ya hau karagar mulki?

An naɗa Alhaji, Dr. Ibrahim Bello a matsayin Sarkin Gusau ranar 16 ga watan Maris, 2015 a zamanin tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul'aziz Yari.

Tun wannan lokacin yake jagorantar masarautar Gusau har zuwa jiya da Allah ya karɓi ransa, ya shafe kimanin shekaru 10 kenan a karagar mulki.

Kara karanta wannan

Sarkin Gusau da wasu manyan sarakuna da suka rasu cikin wata 1 a Najeriya

An mutunta wasiyyar Sarkin Gusau yayin birne shi
An birne Sarkin Gusau kamar yadda ya bar wasiyya. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Yadda aka mutunta wasiyyar Sarkin Gusau a Zamfara

An birne basaraken ne a makaranta sabanin kaburburan sarakunan gida, bisa bukatar da ya nema lokacin da yake raye.

Ahmad ya ce marigayi Sarkin ya yi umarni cewa a birne gawarsa a makabartar jama’a ba a gida ba, cewar rahoton Daily Post.

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tsoron Allah, mai barkwanci, mai karɓar kowa, mai gaskiya da kuma fayyace magana a mulkinsa na shekara 10.

Ya ce:

“Yana nuna soyayya, fahimta, kuma ba ya karya alkawari a mu'amalarsa da jama’arsa."

Tinubu ya yi jimamin rasuwar Sarkin Gusau

A baya, mun ba ku labarin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'azziyar rasuwar Sarkin Gusau, Dr Ibrahim Bello wanda ya rasu a safiyar ranar Juma'a bayan fama da jinya.

Tinubu ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi, yana jinjina masa bisa hidimomin da ya bayar ga al'umma wanda ba za a manta da su ba ko kadan.

Shugaban ya mika ta’aziyya ga gwamnatin Zamfara da dangin marigayin, yana rokon Allah ya jikan Sarkin da rahama, ya ba shi aljanna firdaisu mai daraja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.