Rigiji Gabji: 'Yan Sanda Sun Kama Sojoji a Wajen da ba a Tsammani

Rigiji Gabji: 'Yan Sanda Sun Kama Sojoji a Wajen da ba a Tsammani

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an tsaro sun cafke mutane 22 da ake zargi mambobin ƙungiyar Aiye ne a wani otal a Ogun
  • Bayanin 'yan sandan ya nuna cewa an kama su ne yayin wani samame da aka kai da daddare bisa sahihan bayanan leƙen asiri
  • Legit ta gano cewa cikin waɗanda aka damke akwai mata da kuma sojoji da ake zargin suna da alaka da wata kungiyar asiri

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - Jami’an tsaro a jihar Ogun sun cafke mutane 22 da ake zargi ‘yan ƙungiyar asiri ta Aiye ne a wani otal da ke Osiele, karamar hukumar Odeda.

Wannan samame ya biyo bayan sahihin bayanan leƙen asiri da suka nuna cewa akwai taron ‘yan ƙungiyar da ba bisa ka’ida ba da ake shirin gudanarwa a otal ɗin Hilltop da ke yankin.

Kara karanta wannan

Dakarun tsaro da mafarauta sun hada hannu, an yi fata fata da 'yan ta'adda

Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka kama su ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

Wata majiya ta ce jami’an haɗin gwiwa daga sashen Aregbe, rundunar SWAT da kuma na yaƙi da ƙungiyoyin asiri sun mamaye otal ɗin da daren Juma’a tare da cafke waɗanda ake zargin.

Yadda aka kama sojoji da sauran mutane

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa cikin waɗanda aka cafke akwai mata guda uku da kuma sojoji biyu da ake zargin suna da alaka da ƙungiyar asirin.

An ce jami’an sojin na aiki a halin yanzu, kuma ana ci gaba da bincike kan ko suna da alaka da kungiyar Aiye.

Punch ta wallafa cewa an tabbatar da kama wasu maza guda 19, waɗanda duk ake zargin mambobi ne ko kuma masu hannu wajen gudanar da ayyukan ƙungiyar asirin.

An samu bindiga da gatari a hannunsu

Kayan da aka kwato daga hannun waɗanda ake zargi sun haɗa da wata bindiga, wani babban gatari da kuma riga mai launin shuɗi da ake alaƙanta wa da ƙungiyar Aiye.

Kara karanta wannan

Sojoji sun daƙile mugun shirin ƴan ta'adda, sun kashe mai ɗaukar bidiyo domin yaɗa ƙarya

Majiyoyi sun ƙara da cewa ana ci gaba da tantance sunayensu da cikakken bayani domin gano matsayin kowane ɗaya a cikin ƙungiyar.

Rundunar ta kuma buƙaci jami’an sashen yaƙi da ƙungiyoyin asiri na jihar da ke Eleweran da su ja ragamar bincike a kan al’amarin.

Hafsun tsaron Najeriya, Christopher Musa
Hafsun tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: Defence Headquaters
Source: Facebook

Majiyoyi daga jami’an tsaro sun bayyana cewa gwamnati ba za ta lamunci irin waɗannan ayyukan ba, musamman a cikin al’ummar da ke neman zaman lafiya.

Sun ce duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada, ba tare da la’akari da matsayin sa ba.

An kashe dan bindiga Dan Dari Biyar

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe babban dan bindiga da ya addabi mutane a Sokoto.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe dan bindiga da aka fi sani da Mai Dari Biyar ne yayin da ya shirya karbar kudin fansa.

An bayyana cewa Mai Dari Biyar ba ya tausaya wa mutanen da ya kama domin karbar kudin fansa a yankunan jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng