An Harbe 'Dan Bindiga ‘Dan Dari Biyar' da Ya Shahara da Gallazawa Hausawa
- Rundunar Operation FANSAN YANMA ta hallaka shugaban ’yan bindiga, Dan Dari Biyar, yayin karbar kudin fansa a dajin Sabon Birni
- Dan Dari Biyar ya shahara da mugunta da cin zarafin wadanda suka fada hannunsa sannan ya bukaci kudin fansa mai yawa
- Hakan na zuwa ne yayin da sojoji da jami’an tsaro ke hada kai domin ruguza maboyar ’yan bindigar da suka addabi gabashin Sokoto
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Rundunar sojojin Najeriya da ke karkashin Operation FANSAN YANMA ta samu nasarar hallaka wani shahararren shugaban ’yan bindiga mai suna Dan Dari Biyar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe dan ta'addan ne a wani daji da ke yankin Sabon Birni, Jihar Sokoto.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa Dan Dari Biyar ya gamu da ajalin sa ne a ranar Alhamis yayin da yake kokarin karbar kudin fansa daga ’yan uwan wadanda ya sace.
An ce yana zama ne a matsugunin dajin da ke tsakanin kauyukan Turtsawa, Mazau da Zango a karamar hukumar Sabon Birni.
Muguntar da Dan Dari Biyar yake yi
Dan Dari Biyar da aka fi saninsa da furucin nuna kiyayya ga Hausawa, inda yake cewa 'na fi son ₦500 fiye da Bahaushe' ya dade yana cin karen sa babu babbaka a yankin.
Rahotanni sun ce ya kasance mai nuna tsananin mugunta da wulakanci ga wadanda ya kama kafin ya bukaci kudin fansa mai yawa daga danginsu.
'Dan ta'addan na da sansani a dajin Tidibale
Shugaban ’yan bindigar na da sansani a cikin dajin Tidibale, inda daga nan yake kitsa hare-hare a kan al’umma da ke yankunan Lalle, Tsamaye da Gwaronyo.
An alakanta shi da kona kauyuka da kai wani mummunan hari Gidan Sale a gundumar Gundumi, wanda ya jefa jama’a cikin tsoro da fargaba.

Source: Facebook
An hada gwiwa da jami’an tsaron yankin
Rahotanni sun bayyana cewa aikin ya kasance hadin gwiwa tsakanin sojojin Najeriya da jami’an tsaro na cikin gida karkashin shirin kare al’umma da gwamnatin Jihar Sokoto ta bullo da shi.
Sojoji sun ce farmakin da aka kai wa Mai Dari Biyar ya kasance wani bangare na kokarin da suke yi don kawar da sansanonin ’yan ta’adda a cikin dazuka masu hadari.
An kwato makamai da na’urorin sadarwa
Bayan kashe Dan Dari Biyar, dakarun Najeriya sun gano bindigogi da alburusai da kuma na’urorin sadarwa daga wajen.
Ana ci gaba da bibiyar ragowar ’yan bindigan da suka tsere daga harin, domin tabbatar da cewa ba su sake dawo wa domin yin barna ba.
An kashe 'yan kasuwa 14 a hanyar Filato
A wani rahoton, kun ji cewa wasu mutane dauke da bindiga sun kashe akalla mutane 14 da suke dawowa daga kasuwa a jihar Filato.
Bayanin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa cikin wadanda 'yan ta'addan suka kashe akwai mata da yara kanana.
Wani mazaunin yankin ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa mummunan lamarin ya zo ne a daidai lokacin da suke kokarin tabbatar da zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

